Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farfesa Uche Uwaleke, Daraktan sashen karatun kasuwanci a Jami’ar Jihar Nasarawa kuma Shugaban ƙungiyar Malaman Kasuwancin na Nijeriya ya bayyana cewa, akwai yiwuwar Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara kuɗin ruwa na bashi.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja dangane da taron MPC karo na 298 da aka gudanar a ranakun Litinin da Talata.
A cewarsa, a karon farko cikin watanni da dama, hauhawar farashin kayan masarufi da abinci sun tashi a watan jiya.
“A kowace shekara hauhawar farashin kaya na ƙaruwa wata-wata, yana ƙara faɗaɗa ta kowane fannin.
“Kasuwar canji har yanzu tana fuskantar matsin lamba ta hanyar hauhawar dala. FAAC dai ta raba sama da Naira tiriliyan 1.4 a watan Oktoba, sama da alƙaluman da aka yi a watannin baya,” inji shi.
Ya ce, akwai kuma lokutan bukukuwan da za a yi la’akari da su galibi suna da hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka.
“A kan wannan yanayin, ba zan yi mamaki ba idan MPC ta ƙara yin tsokaci kan MPR da aƙalla maki 50,” inji shi.
Sai dai ya shawarci kwamitin da ya ci gaba da riƙe farashin manufofin hada-hadar kuɗi zuwa matsakaicin farashin saka hannun jari.