Alƙalan Kotun Ƙoli sun koka kan matsalolin da suka addabe su

Daga BASHIR ISAH

Alƙalan Kotun Ƙoli na Nijeriya sun koka kan taɓarɓarewar harkokinsu a ƙarƙashin Babban Alƙalin Nijeriya (CJN), Ibrahim Tanko Muhammad.

A cewar jaridar Peoples Gazette, alƙalan sun bayyana damuwarsu ne cikin wata wasiƙa da suka rubuta suna masu kokawa kan matsalolin da ke addabarsu a bakin aiki, ciki har da rashin kari a kason da fannin shari’a ya saba samu a tsakanin shekaru huɗun da suka gabata.

Cikin wasiƙar tasu, alƙalan sun ce, “Muna yi wa ƙasar nan aiki bilhaƙƙi. Mukan warware matsalolin da suka taso tsakanin Majalisar Zartarwa da ta dokoki, da kuma tsakanin gwamnatoci da ma ɗaiɗaikun jama’a…”

Sun ci gaba da cewa duk da ƙoƙarin warware wa sauran fannoni matsalolinsu da sukan yi, “Zai zama abin takaici idan ‘yan Nijeriya suka san da cewa ba mu iya magance matsalolinmu a cikin gida ba tare da ‘yan waje sun sani ba.”

Haka nan sun ce, sun yanke shwarar sanar da Babban Alƙalin ne a hukmance domin kare martabar fannin shari’a da kuma girman da gwamnati da ma al’umar ƙasa suke ba su.

Matsalolin da alƙalan suka koka a kansu har da rashin musanya musu motocin aiki da suka lalace, rashin muhalli, rashin tsarin kiwon lafiya mai inganci a asibitin Kotun Ƙoli, rashin wutar lantarki da sauransu.

Kazalika, sun koka kan yadda suke fama da tsadar lantarki, rashin intanet da sauransu a wurin aiki ba tare da an yi musu ƙarin alawus da zai taimaka musu wajen rage raɗaɗin matsalolin ba.

Bisa la’akari da yanayin murza gashin bakin da alƙalan suka yi, hakan ka iya haifar wa fannin shari’ar ƙasa cikas muddin ba su cimma buƙatunsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *