Alƙalin Alƙalan Nijeriya ya gargaɗi alƙalai kan rashawa da sharholiya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Babban Mai Shari’a a Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya gargaɗi alƙalan ƙasar nan da su guji tara dukiyar haram domin kauce wa shiga hurumin doka da zai tsumduma su cikin halin ƙaƙa-nikayi.

Mai Shari’a Muhammad ya ce a matsayin su na jami’an shari’a, wajibi ne alƙalai su guje wa hasashe ko hangen tagomashi, rashin gaskiya ko ha’inci da rayuwar fankama ko kece raini da ta yi kama da halayyar masu cin hanci da rashawa.

CJN ya bayar da wannan gargaɗi ne yayin ƙaddamar da wasu alƙalan manyan kotunan tarayyar Nijeriya, da kuma wani guda na babbar kotun birnin tarayya ta Abuja.

Ya bayyana cewar, majalisar lura da lamuran shari’a ta ƙasa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zaƙulo vatagari a cikin ma’aikatar ɗabbaƙa lamuran shari’a ta hanyar yin waje da su.

Mai Shari’a Muhammad ya bayyana cewar, alƙalai masu ta’ammali da cin hanci na iya tsinkewa da gudu, amma ba su iya kauce wa kamun doguwar sandar shari’a ta majalisar kula da lamuran shari’a ta ƙasa (NJC).

“Kamar yadda nake faɗi a kowane lokaci, riƙe madafun gudanar da shari’a baya da nasaba da sharholiya ko wadata, tasiri ko cin albarkaci, ko kuma mummunar alaƙa da zarmammun mutane da za su gabatar wa mutum mabambantan fuskoki, tare da loɓa ka ciki ko kan hanyoyi da suka yi bambaraƙwai ko hannun riga da doka.

“Tilas ne a guji tara dukiyar haram, rashin adalci, da kuma shiga sharo-ba-shanun da mutum zai yi nadamar kasance jami’in shari’a,” ya ƙara da jan kunnuwan su.

CJN ya yi la’akari da duk da cewar, alƙalai ba su da wani iko ko mariƙar igiyar mulki ta musamman da za su gudanar da wata bajinta ta musamman, don haka ya jawo hankulan sabbin jami’an shari’ar da su zage damtse wajen yi wa jama’a bajintar bazata.

Mai Shari’a Muhammad ya kuma roƙi alƙalan da su kasance cikin shirin fuskantar ƙalubaloli, musamman da gabatowar zaɓuɓɓukan gamagari na shekara mai gabatowa, 2023, ya ƙara da duk da cewar, yana taya su murna, yana kuma jajanta masu la’akari da tsegunguma da zarge-zarge da za su fuskanta daga maƙaraya a yayin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

“Babu shakka dukkan mu ajizai ne, amma wajibi ne suke nuna mutum-taka, da wanzar ababe na musamman da jama’a za su yi masu kallon ayyukan gagara badau ne da ba za su iya yi ba.

CJN ya kuma shawarci sabbin alƙalan dasu ƙudura rantsumar aiki da suka yi a cikin zukatan su, tare da yin aiki da hakan a yayin gudanar da ayyukan shari’a.

“Wannan shine alƙawari da za su ƙudurce a cikin zukatan su, da kuma zai kasance jagora yayin zartar da hukunce-hukunce kan ƙararraki ko koke-koke dake gaban su.

“Tilas ne ku tsaya daram bisa hanyar nuna ‘ba sani ba sabo’, adalci da gudun son zuciya. Ba mu buƙatar wani boka ya shaida mana cewar, lokatai masu hatsaruka da nasihai ne.”

CJN ya jaddada cewar, hali ko yanayin da Nijeriya take ciki yana bukatar gogaggun alƙalai masu nagargarun halaye da tarbiyya, kuma masu kamanta gaskiya, masu kyawawan manufofi, masu nitso ko kamala da tawali’u, ya ƙara da faɗin, ɗaukar alqalan cikin aiyukan hukuma ba an yi shi da rashin manufa ba ne, an yi shi bisa zaɓin Allah ne, don haka wajibi ne su nuna hikima tare da jagorancin lamiri ko lura da sharri.

Sabbin alƙalan dai sune Emmanuel Gakko, Musa Sulaiman Liman, Segun-Bello Mabel Taiye, Bala Khalifa-Mohammed Usman, Ahmad Gama Mahmud, Aminu Garba na Babbar Kotun Tarayya da Joseph Adebayo Aina na Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja.