Al-Makura ya sha kaye a zaɓen Sanatan Nasarawa ta Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma Sanata Umaru Tanko Al-Makura, mai wakiltan Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa ƙarƙashin Jam’iyyar APC, ya sha kaye a zaɓensa na sake tsayawa takara a hannun Mohammed Ogishi-Onawo na Jam’iyyar PDP.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a ranar Litinin a Lafiya, babban birnin jihar, Farfesa Ahmed Ashiku, jami’in zaɓen, ya bayyana cewa Ogoshi Onawo ya samu ƙuri’u 93,064 inda ya doke Sanata mai ci Al-Makura wanda ya samu ƙuri’u 76,813.

Ashiku, yayin da yake bayyana cewa Onawo, bayan ya cika sharuɗɗan doka kuma ya samu mafi yawan ƙuri’u, an mayar da shi.