Al-Mustapha ya zargi ƙasashen Yamma da tsawaita ta’addancin Boko Haram

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Ɗan takarar Shugaban Nijeriya a Jam’iyyar ‘Action Alliance’ kuma tsohon jami’in tsaron tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi zargin cewar, akwai wata maƙarƙashiya da ƙasashen Yamma suke yi na tsawaita ta’addancin Boko Haram a ƙasar nan.

Al-Mustapha ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa kan zaɓen shekara ta 2023 da aka gudanar a makon da ya gabata a birnin Abuja.

Ya ce duk da cewar, an ƙyanƙyashe ta’addancin Boko Haram ne a ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 1999, amma an ƙudura aniyyar sa ce tun a shekara ta 1972 bayan da aka gano man fetur da na gas a ƙasar nan.

Al-Mustapha ya zargi ƙasashen na Yamma da shirya kututun rikice-rikice mai ɗorewa a ƙasashen Afurka, kamar su jamhuriyar dimukraɗiyya ta Congo, Mozambique, Libya, da sauran su, wurare da aka tabbatar da samuwar ɗimbin ma’adanai a cikin ƙasa.

Fitaccen jami’in na tsaro ya bayyana cewar, Gwamnatin Tarayya ta gano ɗimbin ɗanyen man fetur da munduwa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin ƙasar nan a shekara ta 1996, wanda ya ce tuni ake ta haƙar su ta varauniyar hanya, yayin da ta’addanci yake ta gudana a waɗannan sassa na Arewacin Nijeriya.

Al-Mustapha ya ce duk da cewar, jihar Borno ita ce cibiyar ta’addancin Boko Haram a Nijeriya, abin mamaki shi ne yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu suke biyan kuɗaɗen hayan matsugunai na kimanin tsawon shekaru 10 zuwa 20, lamarin da ke nuni cewar, akwai wata maqarqashiya na tsawonta ta’addancin.

Kamar yadda ya zayyana: “Jihar Borno wuri ne da ya kamata a guje wa sabowa yadda tashe-tashen bomabomai ke aukuwa. Amma wani zai yi tambayar ko me ke yawanta zamantakewar ƙungiyoyi masu zaman kan su, musamman ma a babban birnin jihar ta Maiduguri. Da matuqar wahala ake samun gidajen haya a birnin, saboda waɗannan ƙungiyoyi sukan karɓi hayar gidaje na kimanin shekaru 10, 18 zuwa 20. Wannan ma wata alama ce na tsawaita zamantakewa.

“Wani zai yi tambayar me ya kawo haka? Su wane ne waɗannan ƙungiyoyi masu zaman kan su? Wane ne ke da alhakin tantance su yana turo su Nijeriya? Wane dalili ne ya sanya sojoji da ‘yan-sanda, hatta duk wani mai sanya tufar hukuma yake tsorace da Nijeriya, musamman jihar Borno?

“Wane dalili ne yake sanya waɗannan ƙungiyoyi masu zaman kan su suke da yakana, masu son yin abotaka da mutane? Yanayin ba mai abotaka ba ne, yanayi ne mai tsauri. Wane dalili ne ya sa suke son yin alaƙa da Borno? Mene ne ya sanya ba su son zuwa wasu ƙasashe dake da zaman lafiya, masu ingantattun yanayi? Waxanne hidimomi suke gudanarwa a jihar Borno? Duka waɗannan tambayoyi ne na sanyawa a zukata.

“Waɗanne daililai ne ke sanya sojoji guje wa farfajiyoyin Boko Haram? Kuma wane dalili ne ke sanyawa Turawa ko fararen mutane, walau mata ko maza suke ta’ammali da ‘yan ta’adda, suke kuma zuwa gare su a maran lokuta ba tare da wani tararradi ba? Don me ya sa ba mu yi masu tambayoyi? Shin Nijeriya kurmi ce ko ruƙuƙi?

“Mun ko san kammu? Mene ne sunayen waɗannan hukumomi da suke tantance su a nan gida? Ta ƙaƙa suke shigowa Nijeriya? Ta hannun jami’an shige da fice, ofisoshin jakadanci, na lamuran cikin gida, ko fadar shugaban ƙasa. Waɗanne irin ayyuka suke gudanarwa?

“Wane irin shagali ne suke ciki da ba su gudun shiga kowane hatsari a tsakanin ‘yan Nijeriya? Wane dalili ne ya sanya tantagaryan ɗan Nijeriya ba ya iya shiga wuraren da suke shiga a cikin wannan ƙasa? Wane dalili ne ya sanya suke tattaunawa da ‘yan ta’adda? Har ma suna lambobin tangaraho na ‘yan ta’adda da laƙanonin yanar gizonsu? Mene ne ya hana mu sanin waɗannan bayanai?

“Tambayar da nake yi a nan ita ce: Suna da haɗin kai ne da jami’ai ko manajojin tsaro? Ko kuma waɗannan hukumomi ne suka bayar da kawunan su? Ko jahilci ne ya kawo haka? Ko kuma sakaci?

Al-Mustapha sai kuma ya yi tuni da cewar, a watan Janairu na wannan shekara ta 2022, ɗaya daga cikin qasashe da ake zargi da gabtarar kadarori a nahiyar Afurka, ta gabatar da tayin zuba jari a fannin ayyukan gona da taimakekkeniya da jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *