Al-Nakba: Falastinawa ba za su taɓa miƙa wuya ga Isra’ila ba – Ambasada Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A rana ta 223 na yaƙin kisan ƙare dangi a akan al’ummar Falastinu, Jakadan Falastinu a Nijeriya Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa, a cikin shekaru 76 da fara gallaza wa al’ummar Falastinu, ba mu manta ba, ba za mu yafe ba.

Al’ummar Falastinawa za su ci gaba da tunkarar mamayar da Isra’ila ke yi, ba za su taba miƙa wuya ba.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar 16 ga Mayu, 2024, ya ce; “A ranar 15 ga watan Mayu al’ummar Falastinu a duk duniya sun gudanar da bukukuwan cika shekaru 76 na ‘Al-Nakba’ da aka yi tsakanin shekarar 1947 zuwa ƙarshen 1948. A wannan lokaci, gungun sojojin Yahudawa na Turai sun nuna ƙabilanci tare da tumɓuke ‘yan asalin Falastinawa daga tsohuwar ƙasarsu ta Falastinu.

“Al-Nakba yana nufin sama da Falastinawa 15,000 ne suka yi shahada. Palastinawa 950,000 ne suka zama ‘yan gudun hijira a Lebanon, Siriya, Jordan, Yammacin Gabar Kogin Jordan, da Gaza, tare da kawar da ƙauyuka da garuruwa 531 daga cikin 1,300 gaba ɗaya. A yau, Falastinawa ‘yan gudun hijira miliyan 5.8 ne aka yiwa rijista.

“Ana ci gaba da bayyana hujjoji da dama, kamar kaburbura, varnata rayukan jama’a, da sauran ta’addancin da ‘yan sahayoniya masu ɗauke da makamai suka aikata a lokacin Al-Nakba. Dole ne mu tuna Al-Tantura.

“A rana ta 223 na ƙazamin yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al’ummar Palastinu, zan so in yi nazari tare da ku; Shahidai 45,091 da suka haɗa da yara 15,103, mata 9,961, ‘yan jarida 142 da ma’aikatan lafiya 492. Vacewar mutane 10,000. 78,404 sun jikkata kuma suka jikkata, tare da kashi 72% na waɗanda abin ya shafa yara da mata ne. Yara 17,000 suna rayuwa ba tare ko ɗaya daga cikin iyayensu ba.

“Masallatai 243 sun lalace. An kai hari tare da lalata Coci 3, an lalata gidaje 86,000 gaba ɗaya sannan 294,000 sun lalace gaba ɗaya, makarantu da jami’o’i 103 sun lalace.

“Asibitoci 33 tare da cibiyoyin kiwon lafiya 54 an tsayar da su daga aiki. Jimillar cibiyoyin kiwon lafiya 160 da motocin ɗaukar marasa lafiya 126 Isra’ila ta lalata su.

“Mutane 11,000 da suka samu raunuka na buƙatar yin balaguro domin neman magani. Masu fama da cutar daji 10,000 na fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin magani. 1,095,000 suna kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa sakamakon ƙaura.

“Mutum 20,000 a wasu lokuta na kamuwa da cutar hanta ta saboda ƙaura. Dubun dubatar mata masu juna biyu na cikin hatsari saboda rashin samun kulawar lafiya. An kama jami’an lafiya 310,” inji Abu Shawesh.