Alaƙar Buhari da Tinubu tana ƙara armashi – Fadar Shugaban Kasa

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya musunta zargin da ake yaɗawa kan cewa ruwa ya yi tsami tsakaninsa da tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Buhari ya musunta zargin hakan ne ta wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar inda ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta nuna cewa, hasali ma alaƙar da ke tsakanin dattawan biyi sai armashi da ƙarƙo take ƙarawa.

A cewar Shehu Garba, “Fadar Shugaban Ƙasa na faɗa da babbar murya cewa babu wani rashin jituwa a tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da na hannun damarsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

“Akwai himma mai ƙarfin gaske a tsakanin Buhari da Asiwaju ga jam’iyyar APC wajen tabbatar da an samar da canji mai inganci, kuma wannan shi ne abin da suka tabbatar za a yi wa ‘yan Nijeriya.

“Rahotannin baya-baya da suka yi ta yaɗa batun rashin jituwa a tsakanin shugabannin jam’iyyarmu, wannan ba gaskiya ba ne shiri ne kawai na mahassada.

“Abin takaici ne ganin yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗa irin labarun da ba su da tushe balle makama, suka bari mahassada na amfani da su wajen yaɗa manufarsu ta ƙarya.”

Garba She ya ci gaba da cewa, “Wannan gwamnatin na sane da ‘yan gutsiri-tsomar da ke yaɗa bayanan ƙarya don kawai su haifar da ruɗani a zukatan jama’a game da shugabanni da kuma makomar jam’iyya.

“Babu shakka, Shugaban Ƙasa da kuma jam’iyya suna kan hanya madaidaiciya don samar da cigaba mai ma’ana, zaman lafiya da ingancin tsaro, daidaita sha’anin tattalin arzikin ƙasa gami da yaƙi da rashawa a ƙasa, kuma babu wani abu da za a yi wanda zai karkatar da hankalinsu ga barin cim ma ayyukan alherin da suka sanya a gaba.

“Asiwaju Bola Tinubu zai ci gaba da zama ɗaya daga cikin ƙusoshin ‘yan siyasar ƙasar nan waɗanda Shugaba Buhari ke martabawa. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kafawa da kuma bunƙasa APC, don haka alaƙar da ke tsakanin su biyun sai sam barka kawai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *