Alamomin ƙurajen da ake hanzarta ganin likita

Daga AMINA YUSUF ALI

Idan ƙuraje suka zo tattare da waɗannan matsaloli, wajibi a dangana da likita. Duk da dai yawanci ƙananan ƙuraje ba abin damuwa ba ne sosai, amma duk wanda ya ke fama da waɗannan alamomin nan, ya je ya ga likita kai-tsaye kawai:

  1. Ciwon maƙogoro
  2. Ciwon gaɓoɓi
  3. Idan wani ƙwaro ko wata dabba ta cije ka gabanin su fito.
    4  Jajayen layuka ko dabbare-dabbare a gefen ƙurajen.
  4. Gefen ƙurajen yana raɗaɗi
    Idan ƙurajen suna ɗurar ruwa
    6  Launin fatar ya canza.
  5. Maƙogoro ya dinga buɗewa da ƙyar tare da jin wahalar numfashi. 
  6. Zafi mai tsanani a ƙurajen. 
  7. Zazzaɓi mai zafi
  8. Kumburin fuska ko na wani waje a fatar.
  9. Tsanannin zafi a wuya ko kai.
  10. Yawan amai da gudawa.

Duk waɗannan alamomin idan su ka zo tare da fesowar ƙananan ƙuraje, zai fi a tuntuɓi likita, domin akwai yiwuwar samun wata matsala a fatar ko a wani ɓangare na jiki.

Zuwan na da matuƙar muhimmanci, domin za a samu damar sanin ainihin abin da ya haddasa su tare kuma da samun damar murƙushe matsalar tun ba ta kai ga zama babba ba.