Alamomin da ke nuna fata ba ta karɓi kayan kwalliyar da ake amfani da su ba (1)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A yau shafin kwalliya zai yi magana ne kan tafiya neman gira da ake yi a ɓangaren kwalliya sai kuma a rasa ido kan hanyar, ma’ana amfani da kayan gyaran fata ba tare da sanin zaɓin fatar ba, wanda lokuta da dama garin neman ƙibar sai kuma a tono rama, maimakon fatar ta yi kyau sai ta kamu da wata cutar.

Sanin abin da fata ke buƙata a kwalliya yana da matuƙar muhimmanci a lokacin da kika ɗaura aniyar sama wa fatarki kyau da ƙyali, domin ta hanyar ilimin ne kawai za ki san abinda zai ciyar da ita gaba da wanda zai iya kaita ga halaka.

Kayan shafa tamkar abinci ne ga fatar jiki, lokacin da take cin wanda ba nata ba za ta iya shiga mawuyacin hali, har ta kai ga lalacewa tare da bayyanar da wasu curuta da ta kamu da su ta sanadiyyar ciyar da ita gurɓataccen abinci.

Hanyoyin da za ki iya gane fatarki na adawa da abin da kike bata kuwa mai sauƙi ne, matuƙar za ki ajiye hankali, domin za ta dinga aiko maki da saƙo tun a farkon fara amfani da su.

Ta yaya za ki gane kayan kwalliyar da kike amfani da su na cutar da fatarki?

Shin kina jin ƙaiƙayi a fatarki bayan kin shafa mata wani mai ko wasu kayan kwalliya, ko ƙananan ƙuraje na fesowar a jikin fatarki bayan fara amfani da wani nau’in mayuka da makamantansu. Fatarki na canza kala ko tayi bore yayin da kike mu’amala da wasu kayan kwalliya. Kina lura da yadda fatarki ke duhu alhali haske ya kamata ta yi bayanan kin shafa mata mai mai tsada ko wasu kayan adon fata. Shin kin taɓa lura da yadda ƙyalin fatarki ke disashewa duk bayan tsantsara kwalliya. Ko kin fahimci yadda kike yawan jin zafin saukar abin da kike shafa wa fatarki na gyara.

Duk waɗannan alamomi ne da ke iya samuwa yayin da kike amfani da kayan kwalliyar da fata bata so. Kawar da kai gare su kan kai ga manyan matsaloli kamar haka;

Bushewar fata tare da ɓarewar fata:
A duk lokacin da kika lura fatarki na bushewa tare kuma da yin saɓa, alama ce ta fatarki na fushi da abin da kike shafa mata, ya Allah mai ne ko fauda ko wasu nau’o’in kayan kwalliya. Wannan matsala za ta iya zama sanadiyyar amfani da kayan kwalliyar da suka yi wa fata ƙarfi ko waɗanda ba na irin fatar ba ko kuma sanya kayan kwalliyar fiye da yadda fatar ke buƙata. Idan kuwa ba a magance ta ba, ta iya ci gaba da girma, ta hanyar ba wa ƙwayoyin cuta damar shiga fatar har ta kai ga cutar da kallon fatar ma zai zama ƙazanta idan ya yawaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *