Daga AISHA ASAS
A satin da ya gabata, mun fara bayyanin yadda kayan kwalliya ke tasiri wurin lalacewar fata da kuma janyo mata matsalolin da ka iya zama wani ciwon na daban. Har muka fara zayyano wasu daga cikin alamomin da idan an gansu a fata to alamu ne na bata aminta da kayan kwalliyar ba. A wannan sati zamu ci gaba ne da kawo wasu daga cikin alamomin har zuwa inda ruwan alƙalamin wannan satin zai tsaya.
Bar-ni-da-mugu:
Da yawa suna ganin matsalar cizon kwari ko tava wani abu da fatar bata amsa na daga dabbobi ko tsiro ne kawai ake iya haɗuwa da ƙurajen da ake kira bar ni da mugu, sai dai za su iya samuwa a yayin da fata take neman ceto daga kayan kwalliya da ake ciyar da ita da su waɗanda a wurin ta guba ne.
Allaji (allergy):
Akwai wasu lokuta da za mu iya cin karo da abin da ba illa ba ne a zahirance, amma na ka jikin sai ya zama tamkar guba gare shi. Za mu iya kiran allaji a matsayin ciwo mai dogon lokaci da mai gajere, domin zai iya kasance wa ciwo da ke taso wa lokaci-lokaci, Ya Allah saboda yawaitar tu’ammali da abin da jikin bai aminta da shi ba, ko zamewarsa ciwo da’imi. Hakazalika, zai iya zama ciwon da kan taso kawai a lokacin da ka ci, ko ka sha ko kuma ka yi tu’ammali da abin da jikin naka ya haramta ma.
A ɓangaren kayan kwalliya ma za a iya samun wannan matsala, ta hanyar cin karo da wani abin shafa da jiki ba ya son ya tava fata ko ba ya son ƙamshinsa da makamantansu. Idan irin haka ta samu, za a iya fuskantar ƙananan ƙuraje da za su bayyana a ko’ina na fatar jiki. Za su haifar da ƙaiƙayi da ma rashin lafiya a wasu lokuta. Shi yasa yake da matuƙar muhimmanci idan an ga alamun yiwar haka, ake saurin tsayawa da amfani da kayan kwalliyar, sannan a nemi masana don tabbatar da zargin tare da sanin matakin da za a ɗauka.
Maiƙon fata:
A kwanakin baya, mun taɓa yin darasi kan yadda jiki yake halitta maiƙon da yake fitowa a fata don hanata bushewa. Idan har ma’abuci karatun Manhaja ne kai, za ka iya tuna wa da darasin yayin da ka yi nazari, idan ka tuna kuwa, mun bayyana ƙwayoyin halittar da ke aikin samar da maiƙon da yadda suke aikin na su da kuma yadda matsala ta fata kan tursasa su tunkuɗo maiƙon da yawa ko kaɗan.
Kayan kwalliya na ɗaya daga cikin matsalolin da ka iya rikita fitowar maiƙon fata. Cikin alamomin da fata zata iya bayyana wa a ƙoƙarin nuna ƙiyawa ga kayan kwalliya akwai bushewar fata. A duk lokacin da kika lura da yawaitar bushewar fatarki fiye da yadda kika saba yi, to ki fara da zargin kayan da kike amfani da su na kwalliya ta hanyar tsayar da amfani da su don tabbatarwa.
Matsalar da bushewar fata ka iya kawowa baya ga rashin jin daɗin jikinki akwai rikitar da sinadarin da ke halitta maiƙon. Dama yakan yi amfani da yanayin fata ne lokacin da yake aiko da maiƙon. Idan fata na bushewa fiye da yanayinta ba zai dubi ciwo ne ba, sai ya ƙara giyar gudun aikinsa, ya dinga yin ambaliyar maiƙon a ƙoƙarinsa na ganin ya raba fata da bushewar da take. Sai dai ba zai yi nasara ba, saboda a duk lokacin da ya tunkuɗo, wannan matsalar sai ta haɗiye a ƙoƙarinta na ganin ba a ɓata mata shirinta na kawo matsala a fata ba.
Shima a ɓangaren wannan sinadarin, hakan na da matuƙar illa gare shi a gaba, domin komai ake ɗiba fiye da yadda aka tsara shi zai iya samun matsala a gaba.
Amya:
Wasu nau’o’in ƙuraje ne da suka fi kama da na cizon kwaron zuma, wani lokacin sukan zo irin ɗaya daga cikin ƙurajen da mai allaji ke yi waɗanda suke da mabambantan kamanu. Sukan fito kamar na ƙonewar wuta, sai dai su ba sa baƙi, ko su fito ba tare da ƙurji ko ɗaya ya fito ba ta hanyar yin ja, ma’ana, fatar kawai za ta yi jawur. A duk lokacin da kika fahimci wannan a fatarki, to ki gaggauta ajiye kayan kwalliyar da kike amfani da su na ɗan lokaci don ganin ko su ne sanadin fitowar su.
Shawara:
A lokacin da kika sayi sabbin kayan kwalliya, kada ki fara shafa wa fatarki har sai kinyi gwaji ta hanyar shafa kaɗan a wani gurbi ƙarami na hannunki tsayin wuni, idan kika lura wurin na ma ki ƙaiƙayi ko ya canza launi ko lura da yanayin fatar ya canza zuwa yanayin da ba a so, sai ki guje masu tun ba ki fara ba. Ba lallai ba ne ki iya gane hakan a shafawa ɗaya ba, don haka na ke ba ki shawarar ki maimaita hakan tsayin kwanaki uku kafin ki tabbatar da amfani ko rashin gamsuwa da tasirin su ga fata.