Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Barcelona da Jordi Alba sun cimma yarjejeniyar raba gari tun kan kwantiraginsa ya ƙare a ƙungiyar.
Alba, mai shekara 34 ya koma Camp Nou a 2012 daga Valencia, ya kuma lashe La Liga shida da Copa del Rey biyar da gasar Zakarun Turai a 2015.
Ya buga wa Barcelona wasanni 458 har da 29 a kakar nan da ƙungiyar Camp Nou ta ɗauki La Liga na bana na 27 jimilla.
Alba ya zama na biyu da zai bar Barcelona a aarshen kakar nan, bayan kyaftin, Sergio Busquets.
Barcelona ta kai ga cimma wannan matsaya, bayan da ta ke son cika ƙa’idar La Liga ta kashe kuɗi daidai samu, wato financial fair play.
Barcelona ta sayar da Lionel Messi bayan da ta faɗa matsin tattalin arziki, wadda daga baya ta nemi kuɗin sayo wasu ‘yan qwallon har da Jules Kounde daga Sevilla.