Alena: Baƙar fata ma fi ƙarancin shekaru da ta samu gurbin karantar fannin likitanci

Alena Analeigh Wicker mai shekaru 13 ta kasance ɗaliba baƙa ta farko da ta fara samun gurbin karatu a fannin karatun likita a yayin da take shekaru 13 kacal a Duniya.

Alena Analeigh Wicker ita ce ɗaliba baƙa ta farko da ta aka fara amsa a fannin karatun likitanci a Duniya.

Ita dai wannan ‘yar yarinya wacce ta fito daga garin Fort Worth na Texas ta Amurka ta kasance tana karance-karance tun tana ‘yar shekara 3.

Sannan ta yi kwasa-kwasai na share fagen jami’a yayin da take shekaru 11 kacal. Sanna ta shiga kwalejin tana shekara biyu domin samun karatun digiri a fannoni biyu mabanbanta.

“Wai ma menene shekarun?” Tambayar da ɗalibar likitanci Alena ta yi yayin tattaunawarsu da ‘yan jaridu.

Inda ta ƙara da cewa: “Ba wanda ya yi ƙanƙanta don yin wani Abu. Ni yanzu ina jin na ba wa kaina tabbacin cewa zan iya yin duk wani abu da na sanya zuciya a kai”

Haziƙar matashiyar da ma ta kasance koyaushe tana yi wa sa’o’inta fintinkau a kan dukkan wasu fannonin na rayuwa. Amma ta bayyana cewa, a zuciyarta ba ta jin ta fi kowa. “Har yanzu dai ina nan a matsayinsa na yarinya ‘yar shekaru 13” , inji ta.

A cewar Alena, bayan karatu da take mugun so, tana kuma sha’awar zuwa kallo a silima, wasan ƙwallon ƙafa, gashe-gashen kayan maƙulashe da kuma yawo da ƙawaye.

Alena ta bayyana sirrin wannan nasarar tata da kasancewarta gwana wajen iya sarrafawa da tattalin lokacinta.

Sannan Mamanta wacce ta taimaka mata ba don ita ba a cewar ta, ba za ta iya samun wannan nasara ba.

Alena a halin yanzu ɗaliba ce a a jami’o’in Arizona State University da kuma Alabama’s Oakwood University inda take karatun digirinta guda biyu a fannin halittar ɗan’adam. Wanda yawanci a yanar gizo take karatun.

Iyaye da malamanta su suka fara ba ta shawarar ta nemi girbi a fannin karatun likita inda ta nemi gurbin karatun a Fannin karatun likitanci na Heersi dake a jami’ar Alabama’s Heersink zuwa shekarar 2024.

Sai dai a watan Mayun shekarar nan aka ba ta gurbin karatun duk kuwa da shekarunta sun gaza na sauran ɗaliban da shekaru 10.

Wannan ya nuna ta tsallake rijiya da baya sosai. Domin bayan ƙalubalen shekaru da take fuskanta, akwai ƙalubalen kasancewarta baƙar fata ma zai iya kawo mata tazgaro wajen samun gurbin karatun.

Daphne McQuarter, mahaifiyar Alena ta bayyana cewa, tun tana yarinya Alena yarinya ce mai wayo da basira. Saboda bakin mutane a kan wayonta da basirarsa sun yi yawa ya sa ta cire ta a makaranta ta cigaba da koya mata karatu a gida. Sai daga baya ta mayar da ita makaranta.

A halin yanzu Alena ta amshi kyaututtukan da lambobin yabo kala-kala a kan harkar karatun kuma yanzu babban fatanta a cewar ta shi ne, ta zama ƙwararriyar likita a yayin da ta cika shekaru 18 da haihuwa.