Alfanun tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A baya mun duba tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen, da dalilan da suka kai su in ma ta hanyar fatauci ne, ko cinkayyar bayi. Baya ga haka mun ga ire-iren ƙasashen da suka je kamar Tiripoli da ke Libiya da Chadi, da Turai kamar kudancin Amurka da suka haɗa da Brazil da sauransu.

A bisa kyakkyawan bincike da nazari, duk inda aka samu wata al’umma tana gudanar da harkokin rayuwarta to, nan ne take tafiyar da al’amuran rayuwarta da suka haɗa da al’adunta da amfani da harshenta wanda shi ne harshen adabi mai nuna irin azancinta da fasaharta da irin jawo hankalin jama’arta da ta ke yi da shi. A lokacin tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen wajen fatauci, da cinikayyar bayi. Bai hana su gudanar da al’adunsu na yau da kullum ba, kamar yadda suke yin su a ƙasashensu na haihuwa ba.

Haka zalika, idan aka duba ɓangaren al’adun Hausawa, za a ga cewa Hausawa sun riƙa tafiyar da harkokin addininsu na Musulunci kamar yadda ya kamata babu tsangwama a wasu ƙasashen. Misali, shashin malami ferfesa Abu Manga a muqalarsa da ya gabatar ya nuna cewa, Hausawa sun samu kyakkawar mu’amala ta fuskar zamantakewa da Larabawan Sudan da Fulani da sauran ƙabilun da suka samu a ƙasar Sudan. Ire-iren alfanun da Hausawa suka kai Ƙasar Sudan akwai al’adun da suka shafi bukukuwan salla da ta haɗa da babba da ƙarama, sannan akwai al’adun aure da nemansa, kai bai tsaya nan ba sai da ya nuna cewa hatta nau’in cimaka ta Hausawa sai da ta samu karvuwa a wannan ƙasa a wancan lokaci. Ya nuna cewa, Musulunci ya taka muhimmiyar rawa ta hanyar ɗinke zumuntar da ke a tsakanin wasu sauran ƙabilun ƙasar da su ma suke a can kamar Bare-bari da jula da Wangarawa da Fulani da dai sauransu.

Bayan haka, wasu sana’o’in hannu na gargajiya na Hausawa duk an kai su irin waɗannan ƙasashe sanadiyar zuwan Hausawa can. Game da sarauta irin ta gargajiyar Bahaushe, har can ma ta je. Misali a Wajen shekara ta 1920 da sarkin Katsina Muhammad Dikko ya dawo daga Ingila sai da jirginsu na ruwa ya tsaya a Sakunde ta ƙasar Ghana. A nan ne sarkin Hausawan Kumasi, malam Sallau Ɗan Yakubu, Bakatsinen garin Kusada, da limaminsa da wasu Hausawa suka zo suka gaishe da sarkin. Haka kuma, a lokacin da sarkin Katsina ya je Akara ma sai da sarkin Hausawan garin da limaminsa Mazawaje suka je suka gaishe shi, irin gaisuwar Hausawa.

A vangaren haɗa auratayya Hausawa a waɗancan ƙasashe sun haɗa jinsi ta fuskar auratayya, inda aka samu wasu Hausawa da suka rinqa auren matan al’ummomin waɗannan ƙasashe. Yin hakan ya kawo haɗa al’adun Hausawa da wasu al’adu waje ɗaya wanda kuma ya kawo yaɗuwar al’adu da ɗabi’u na Hausawa kuma yana daga cikin abin da ya bunƙasa al’adun Hausawan. Hatta sanya tufafi irin na Hausawa da yin amfani da harshen Hausa sai da suka yi tasiri a waɗancan ƙasashe. Sannan sun samu cikakkiyar karɓuwa a waɗancan ƙasashe.

Hausawa da inda suka samo sunan Hausa-Fulani:

A baya a cikin shimfiɗa mun ga wane ne Bahaushe? Da addininsa na gargajiya kafin zuwan Musulunci da bayan ya karɓi Musulunci. Sannan mun ɗan yi tsokaci a kan tafiye-tafiyensu zuwa wasu ƙasashe na duniya waɗanda suka haɗar da ƙasashe na nesa da na kusa.

A jiya da kuma yau za mu cewa Hausawa da Fulani kamar kai ne da fata ko kuma jini ne da tsoka kusan a wasu lokuta ba sa rabuwa, ma’ana akwai alaƙa tsakanin Hausawa da Fulani ta auratayya fiye da kowacce ƙabila da ta ke zaune kusa ko kuma nesa da Bahaushe. Fulani kamar sauran al’ummomi ne, suna da addininsu na gargajiya da camfe-camfe da suka mayar da shi hanyar bautarsu kafin su karvi addinin Musulunci. Su wane ne Fulani? Fulani al’ummomi ne masu son zaman lafiya da kyakkyawar ma’amala ta zamantakewa, mutane ne masu kunya da ƙara da kawaici da sanin yakamata da zumunci da son juna da son zaman lafiya da makwabtaka kyakkyawa. Duk inda Bafulatani yake babu abin da ya sa gaba sai sha’anin gabansa, misali mazaje su tafi kiwo, matayensu su tatsi nono da madara su shigo gari su sayar. Ina ne mazaunin Fulani? Kusan duk duniya babu inda ba Fulani, wani masani yana cewa duk inda ka ga makiyayi da dabbobi a jeji Bafulatani ne, don haka ma iya cewa akwai Fulani a Turai da Afirka da Latin Amurka da Asiya da kuma yankin Austriliya da yanki Papua. Akwai wani bincike da aka gabatar da ya nuna cewa an gano waɗansu Fulani a dajin Pansilbeniya da ke Amurka da Jihar Tadik inda suke zaune da Busashensuda matansu da ’ya’yansu. An tattauna da su da yadda suke gudanar da rayuwarsu da karatun ’ya’yansu.

Fulani wayyayu ne domin addini ya taka muhimmiyar rawa wajen wayewarsu. Bayyanar addini da ilimi shi ne matakin farko na samun daraja da mutunci ga Fulani a qasar Hausa. Samuwar malamai da littattafai da ɗalubai ita ce alamar bunƙasar ilimi ga yanki ga ƙasa. Abubuwa masu bin waɗannan su ne makarantu da masallatai. Waɗannan abubuwa su ne suka ƙarfafa Fulani a ƙasar Hausa musamman a lokacin Daular Usumaniyya.

Abubuwan da suka ƙarfafa alaƙar Fulani da Hausawa a zamanin Dauri:

  1. Karantarwa
  2. Addini
  3. Kasuwanci
  4. Auratayya
  5. Karantarwar tarihi ya nuna cewa, Fulani sun yi Laura daga ƙasashe da dama sun shigo qasar Hausa domin karantarwa, irin waɗannan ƙasashe sun haɗa da Sinigal, da Gambiya da kuma Mali. Misali a Kano Fulani sun zauna a Gabasawa/Gezawa, garin Zangon xan Ashura a duba Raliya (2019) a littafinta ‘Humble Begini’ da kuma yankuna ko unguwanni da suka haɗa da Yakasai, Gwangwazo, Adakawa da sauransu.
  6. Addini shi ma muhimmiyar hanyace da ta haɗa alaqa tsakanin Hausawa da Fulani. Kamar yadda muka sani Fulani sun karɓi addini suma a kusan qarni na 9, ko 11. Sannan suka ci gaba da yaɗa shi da kuma koyar da shi, har suka zo ƙasar Hausa inda waɗansu suka zama Fulanin gari wato Fillanci ya qare (wato saniya ita ce Fillanci in babu ita Bafulatani sai ya dawo) don haka sai suka zama malamai masu koyar da addini a wancan lokaci da haka ne ma aka samu Fulanin gari malamai da na jeji makiwata. Kuma wannan addini ne ya ƙara kula alaƙa mai qarfi tsakanin Fulani da Hausawa a wancan lokaci.
  7. Kasuwanci, ita ɗaya ce daga cikin hanyoyin da suka ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanin Hausawa da Fulani. Kamar yadda muka sani Fulani Mazajensu makiyaya ne masu kiwo, matayensu kuwa sana’arsu sayar da nono da madarar shanu da kuma manshano. Don haka idan Bafulatani yana buƙatar wani abu a hannun Bahaushe sai a qulla cinikayyar ta hanyar ba in gishiri in ba ka manda kafin zuwan kuɗi.