Alfanun zuwan Turawa ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wannan cigaba ne daga rubutun makon da ya gabata.

Duk da cewa, Bature ya zo ya samu Bahaushe da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauransu.

Amma duk da irin wannan cigaba da Bahaushe yake da shi kafin zuwan Turawa, an samu ƙarin cigaba a fannonin da dama sakamakon zuwan nasu. Wannan cigaban kuwa ya sauya yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na rayuwa kusan baki ɗaya sai dai ‘yan abubuwan da ba za a rasa ba.

Idan muka kalli yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na rayuwa da suka haɗa da sufuri ta hanyar amfani da jaki, doki da raƙuma wasu lokutan ma a ƙasa da kuma kwale-kwale a cikin ruwa da sauransu, za mu gamsu cewa lallai Bature ya zo da cigaba ta yadda a yau ana maganar keke, babur, mota har zuwa jiragen ruwa da na sama. Saboda haka za mu bibiyi waɗannan cigaba da Bature ya zo da su daki-daki.

Ɓangaren Sufuri:

Da Bature ya zo ƙasar Hausa, farkon abin da ya fara yi shi ne canja salo da kuma yanayin yadda ake gudanar da sufuri daga tsohuwar hanya wacce take cike da jinkiri da wahalhalu zuwa hanyoyi mafiya sauƙi da kuma sauri.

Bature ya zo ya samu Bahaushe yana amfani da raƙuma, shanu, da jakuna wajen gudanar da sufuri ta cikin rairayi da kwazazzabai da sauransu. Sai ya shimfiɗa hanyoyin jiragen ƙasa da kuma titunan mota domin samun sauƙin ɗaukar kayayyaki zuwa Turai.

Ruwan Sha:

Ruwan sha, yana daga cikin abubuwan da Bature ya inganta. Bature ya samu Bahaushe yana shan koma wannen irin ruwa ne; rijiya, tafki, kwazazzabo, kogi, da sauransu kuma daga tukunya zuwa baka, abin nufi shi ne cewa daga an ɗebo ruwa sai kawai a sha. A wasu yankunan ma na karkara, za ka taras cewa a waje guda ake shan ruwan tare da sauran halittu.

Zuwan Bature shi ne ya zo da ruwan famfo wanda ake dafa shi a zuba masa sinadarin alimin, a tace sannan a sha.

Kiwon Lafiya:

Fannin kiwo lafiya shima yana daga cikin fannonin da Bature ya sabunta tare kuma da faɗaɗawa. Hanyar da Bahaushe yake warkar da cututtuka idan an kamu da su, ita ce hanyar da aka kira maganin gargajiya. Wanzamai, mahauta, maƙera da masu dawa, wato mafaruta, su suke bayar da magunguna a ƙasar Hausa. Wanzami shi ne likitan gama-gari, maƙera suna bayar da maganin wuta, mahauci yana bayar da maganin rauni, sannan kuma sai mafarauta da suma suke bayar da magani gama-gari.

Zuwan Bature shi ne ya zo da asibiti, wanda a cikinsa ya riƙa bayar da magungunan cututtuka masu yaɗuwa, sannan kuma ya riƙa yin riga-kafin kamuwa da wasu cututtukan da suka haɗa da kuturta, cutar kurkunu da sauransu.

Wannan cigaba da Bature ya kawo a fannin lafiya ya kai har ana iya feɗe mutum, a cire masa cuta, a mayar a ɗinke.

Hasken wutar lantarki:

Hasken wutar lantarki da kuma makamashin girki. Kafin zuwan Bature, Bahaushe yana amfani da itace, kara, ciyawa da sauransu wajen samar da haske da kuma makamashin girki. Sai kuma amfani da yake yi da ƙaramin kasko, man gyaɗa da auduga wajen samar da fitila.

Zuwan bature ya zo wa da Bahaushe da man kananzir, iskar gas da sauransu wajen samar da makamashin girke-girke. Sannan kuma yake amfani da ruwa, kwal da sauransu wajen samar da haske. Ta wannan fanni na samar da haske yanzu ya kai ga yana iya zuƙar hasken rana ya mayar da shi fitila, da kuma iska mai juyawa da saurnsu.

Fannin Gona

Haka nan idan muka ɗauki aikin gona, kafin bayyanar Bature, Bahaushe yana amfani da ƙarfinsa da kuma Saniya wajen gudanar da ayyukan gona. Zuwan Bature shi ya kawo amfani da injina da suka haɗa da taraktocin noma, da sauransu waɗanda suka faɗaɗa aikin gona sannan kuma suka sauƙaƙa wahalhalun da ke cikin aikin.

Kayan Alatu:

Kayan alatu su ne kayayyakin more-rayuwa dana kwalliyar jiki da muhalli da sauransu. Bature ya cika Ƙasar Hausa da kayan alatu kamar irin su radiyo, talabijin, firinji, fanka, da sauran na’urori da yau suka mayar da duniya a tafin hannu kamar tauraron ɗan’adam, wayar hannu, kwamfuta da kuma Intanet.

Sadarwa:

Sadarwa na nufin musayar saƙonni. Tsohuwar hanyar sadarwar Bahaushe cike take da jinkiri, wahala da kuma rashin isa nesa. Bature ne ya zo da radiyo, talabijin, tarho, tangaraho, wayar hannu da kuma uwa-uba Intanet.

Sana’o’i:

Zuwan Bature Ƙasar Hausa, ya kawo sababbin sana’o’in da a baya babu su. kafin zuwan nasa Ƙasar Hausa kowace sana’a gadon ta ake yi. Wannan dalilin ne ma ya saka za ka samu wasu gidaje, unguwanni da kuma garuruwa a Ƙasar Hausa da suka keɓanta da wata sana’a ta musamman. Misali, idan ka ɗauki sana’ar jima, duk gidan da sana’ar mai gidan ta zama jima, za ka taras cewa, ‘ya’yansa ma ita ce za ta zamar musu sana’a. Idan aka samu irin waɗannan gidaje suka yawaita, to sai unguwar ta zama unguwar masu jima, kamar yadda ake da wata unguwa a cikin birnin Kano mai suna Majema. Haka nan kuma akwai wani gari da ya yi fice a sana’ar jimar fata a cikin qaramar hukumar Ɗambatta da ke cikin jihar Kano.

To zuwan Bature sai ya zo da Karatun Boko wanda ya samar da ƙarin sana’o’i da suka haɗa da gyare-gyaren na’urori, aikin likitanci, aikin karantarwa, aikin jarida da sauransu. To duk wanda ya je makaranta ya yi karatu kuma ya ƙware a wata sana’a, wannan ita ke zama sana’arsa. Wannan kuwa dama babu ita bare a gada. Sai dai yanzu da ake gadon wasu daga cikin sana’oin da Bature ya zo da su, misali, gyaran ababen hawa.

Ilimin Zamani:

Ilimi zamani shi ne Ilimin Boko. Duk da cewa, tun kafin zuwan Bature, Bahaushe ya iya karatu da rubutu cikin Harshen Larabci. Har ma ta kai shi ga cigaban da ya ari harrufan Larabcin ya sarrafa su yake rubuta Hausarsa da su wanda aka yi wa laƙabi da Rubutun Ajami.

Zuwan bature, ya zo wa da Bahaushe da wani sabon ilimin wanda ya zo masa da sababbin sana’o’i tare kuma da canja yanayin zamantakewar Bahaushe ta hanyar ɗaukaka darajar wasu mutane waɗanda a dauri ba komai bane.

Kafin zuwan Bature Ƙasar Hausa, sana’o’i gadonsu ake yi. Shi ne ma dalilin da ya saka har yau ɗin nan (2018), idan ka je wasu garuruwan Ƙasar Hausa za ka samu unguwanni da gidaje da ma garuruwa da suka kevanta da wasu sana’o’i. Misali, a cikin ƙwaryar birnin Kano akwai unguwanni Dukawa, Karofi da kuma Majema. Su dukawa kuwa su ne masu sarrafa fata bayan an jeme ta. Karofi kuwa a nan ake rini ko tirin kaya. Majema kuwa unguwa ce ta masu hada-hadar fatar dabbobi tun daga saye da sayarwa har zuwa jeme ta a gyara.

Amma da bature ya zo, sai mutum ya je makarantar boko ya yi karatu sannan ya zavi sana’ar da ta dace da shi. Wannan ita ce ta bai wa jama’a da dama damar kai wa wasu matakai na rayuwa.

Shugabanci da Jagoranci:

Zuwan Bature ya kawo sauyi game da yadda ake naxa shugabanni a Ƙasar Hausa. Kafin zuwan nasa, shugabanci gadonsa ake yi shima kamar sana’a. Amma da Bature ya zo, sai lamarin ya sauya. Lamarin sai ya koma gwargwadon hazaƙarka da ƙwazonka da karatunka, gwargwadon irin abin da za ka zama a cikin al’umma.

Amma kafin zuwan Bature Ƙasar Hausa, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.