ALGON ta gargaɗi kwamitin Abba Gida-gida kan zafafa siyasa a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON), reshen Jihar Kano ta bukaci Kwamitin Karɓar Mulki na Jam’iyyar NNPP na jihar da ya daina zafafa siyasa da haifar da tashin hankali ko furta kalaman da ka iya haifar da hargitsi.

Shugaban ALGON na jihar, Bappa Muhammad ya yi kiran ne a sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kan zargin karkatar da kuɗaɗen al’umma da kwamitin ke yi wa shugabannin ƙananan hukumomin jihar domin bayar da tallafin ƙarashen zaɓen da ke tafe nan gaba.

Haka dai na zuwa be bayan da Kwamitin Karɓar Mulki na Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar da manyan ma’aikatansu da su guji bari ana amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumominsu ta hanyar da ta saɓa wa doka.

Shugaban Kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ya ce gargaɗin ya zama dole domin kuwa sabuwar gwamnatin ba za ta lamunci yin almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano ba.

A cikin wata takarda da Babban Sakataren Watsa labarai na zaɓaɓɓen gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Baffa Bichi ya ce, “Mun sami labari cewa ana shirin amfani da kuɗaɗen aananan hukumomi wajen kammala zaɓuka a inda ba su kammala ba, a wasu ƙananan hukumomin Jihar Kano, wanda yin hakan ba dai-dai ba ne kuma ya saɓa wa doka.”

Abdullahi Bafa Bichi ya ce, gwamnati mai jiran gado a jihar ba za ta bari a ɗauki kuɗaɗen al’umma a yi wa wata jam’iyyar siyasa aiki ba.

Amma a martaninta ƙungiyar ta yi kira gare shi da ya yi aiki da hankali domin irin wannan tashin hankalin jama’a ba zai iya tasowa ba a wannan tafiyar ta dimokuraɗiyya.

“An saba yin irin waɗannan zarge-zargen a duk lokacin da aka samu sauyin a shugabanci.

“Muna so musamman mu tunatar da mai yin waɗannan zarge-zarge game irin hakan da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2014 na yin amfani da kuɗaɗen al’umma da ya karɓo daga ƙananan hukumomi 44 da aka yi wa shugaban ƙasa buri.

“Idan dai za a iya tunawa dai an yi zargin an karɓo maƙudan kuɗaɗen har Naira miliyan 70 daga kowacce daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar ba bisa ƙa’ida ba, wanda har yanzu shari’ar tana gaban hukumomi, ta ki da cin hanci da rashawa’’.