Allah ya jiƙan Gumi babba da Gumi ƙarami

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya rahamshe shi, uba ne gare ni sakamakon kasancewarsa aboki na ƙut-da-ƙut ga mahaifina. Sun yi karatu tare kuma sun fito daga yanki guda, sunayensu guda, ɗaya mutumin Gumi xaya kuma mutumin Furfuri. Allah ya sada su da rahamarsa.

A shekarar 1989, na yi tattaki daga Kano zuwa Kaduna har gidan Malam Abubakar Gumi da ke Modibbo titin Adama Street, inda na samu ganin sa, na gabatar da kaina domin bai san ni a zahiri ba, sannan na miqa masa buƙatata, ya yarda ya sa min hannu na ya zame min wakili (guarantor) Ina neman wata jami’a a ƙasar waje. Nan take ya saka min hannu, duk da cewa ni ba ɗan izala ba ne, ba na bin kowacce ƙungiya (saɓanin malaman yanzu da sai ka na ƙungiya za a saurare ka), sannan ya yi wa mahaifina addu’a ya kuma saka min albarka.

Shi kuma Ahmad Gumi ban taɓa ganinsa ba a zahiri kawo yanzu. Amma a shekarar 2002, na yi azumi a Kaduna, kuma a wancan lokaci ni ma’abocin sauraron tafsirai na malamai ba tare da la’akari da wacce ƙungiya suke ba. Wannan ya sa a kullum na kan saurari wa’azin Ahmad gumi da wani malamin ɗarika na Tudun Wada, Ɗan Almajiri. Jefi-jefi na kan saurari na ‘yan Shi’a da ake sawa ko na Ɗangungu. Wannan azumi da na yi a Kaduna, ya matuƙar taimaka min wajen nesantar ƙungiyoyin addini, saboda a kullum babu abinda su ke watsawa fiye da rabuwar kai.

Sakamakon yadda a kullum Ahmad Gumi ke far wa ‘yan ɗarika da kiran su ‘yan bidi’a da kuma ’yan Shi’a waɗanda yake gani ba Musulmi ba, ya sa na daina sauraron sa kwata-kwata, saboda gabar ta kai intiha yadda take ba ni mamaki. Wallahi ban taɓa zaton za a wayi gari da cewa zan yi rubutu na kare Ahmed Gumi ba, domin yadda yake nuna ƙiyayya ba za ka tava tsammani zai dawo ya ajiye makamansa ba. 

Shi kuwa Ɗangungu, wanda shi ma ɗan Izala ne asali, tasa ƙungiyar ta mabiya Ƙur’ani zalla, kullum zancensu shi ne na cewa hadisi gabaɗaya ba shi da wani tasiri a addinin Musulunci. Abinda shi ma ya yi karo da fahimta ta, duk da cewa na yarda akwai hanyoyi da za ɗora hadisai a kan sikeli domin tantance su ba kawai domin Buhari da Musulimu sun ruwaito ba.

Kowa ya san cewa Abubakar Gumi, tare da taimakon Sardauna, su ne waɗanda suka kawo Izala Arewacin Nijeriya, kuma duk da cewa tun kafin zuwan izalar akwai rashin jituwa tsakanin ɗariƙun sufaye, musamman Ƙadiriyya da Tijjaniya. Ba na mantawa muna makarantar kwana, tunda a gidanmu na taso muna yin koabalu, abinda shi ne banbarakwai a wancan zamani, idan zani masallaci na kan saka babbar riga domin na boye ƙabalu na.

Watarana wani a kusa da ni ya ankaro ni, ya yi wuf ya cafki hannu na da zummar sai ya sauke, ni kuma na ƙi, muka yi ta kokawa a haka har aka gane. Ka zo ka ga yadda wasu suka tsangwame ni. A da har zubar da jini hakan ya kawo a Arewa amma yanzu abin ya zama ruwan dare. Me ya kawo haka? Wayewa ta ilimin addini.

Haƙiƙa ina yi wa Abubakar Gumi kyakkyawan zato saboda yadda ya rayu saɓanin malaman Izala na zamani. Rayuwarsa a aikace ta wanzu ba a baki ba. Domin muna da labarin zakkar Isyaka Rabiu da ya ce a maida ta Kano, amma daga baya ya sahale nan take aka rabarwa matalauta ba tare da ya ɗauki wani abu ba. Sannan kowa ya san lokacin da ya ci gasar Sarki Abdulaziz da kuɗi Riyal 250,000 (a yanzu sama da Naira miliyan 75) wadda ya rabar daga Jidda zuwa Najeriya ba tare da shiga da ita gida ba.

Wane malamin Izala yau zai iya rabin haka? Malaman Izalar zamani da za su yi gungu su je mubayi’a ga Ganduje saboda ana zarginsa da cusa Dala, har su riƙa kawo labarin cewa yadda Allah ya wanke Aisha daga zargin zina, haka su ke sa ran za a wanke Ganduje, SUBHANALLAH! Malaman da ke ɗauko kwangilar takarar siyasa su tallata ta a minbarinsu?

Kamar yadda na faɗa a baya, rayuwar Abubakar Gumi na cike da tsantseni da tsoron Allah sannan mutum ne mai sauƙin kai da hangen nesa. Na tuna lokacin da a wajen tafsirinsa aka ce ya kafirta, nan take ya sabunta kalmar shahadarsa.

Sannan ya fito ya ce “Yin zaɓe ya fi sallah” inda aka yi masa ca, haka kuma ya assasa yan arewa su shiga aikin banki kuma a yi ta’ammali da ruba (wanda wasu suke ganin cewa ruba ce) kuma ya ba da sassauƙar fatawa na cewa ana iya cin mushe lokacin tsananin buƙata idan babu mafita. Wannan ya nuna wayewarsa da hangen nesa yadda ya hasaso cewa siyasa da aikin banki za su zama abubuwa biyu mafi mahimmanci a Arewa nan gaba.

Akwai mai ja da hakan a yanzu?. Amma magadansa, sai suka rungumi tsanani, da watsi da faɗaɗa tunani da rashin haƙuri da sabanin fahimta wanda ya jawo mana koma-baya iri-iri, musamman na Boko Haram.

Ƙasar Saudiyya ta gane kurenta na cewa barin malamai masu zazzafan ra’ayi na ci gaba da jan akalar qasar ba zai zame musu mafita ba nan gaba, domin sun ga yadda tsatstsauran ra’ayi irinsu na Bn Laden, ya haifar da ta’addanci a akasarin ƙasashen duniya. Malamai su rika cewa muryar mace al’aura ce, mace ba za aifi a ce jinin ka ya halatta da sauransu. Yanzu sun gano cewa dole a bar sassaucin da addini ya zo da shi ya yi aiki.

A nan Nijeriya, ko ka ƙi ko ka so, irin waxancan fatawoyi masu tsauri, musamman da malam Jafar ya yi ta koyarwa a Maiduguri tsawon shekaru, ita ta haifar da su Muhammad Yusuf, waɗanda suka zama Boko Haram. Ko’ina a duniyar musulmi, kama daga ISIS a gabas ta tsakiya, ISWAP a yammacin Afirka da AL-SHABBAB a gabashin Afirka, tabbas za ka same su gyauron Izala ne (Wahhabiyanci).

Ahmad Gumi, ya gane wannan illar, kuma Allah ya yi masa ni’imar ya iya fitowa fili ya nuna cewa dole a maido da sassaucin addini tare da haɗa kan musulmi. Wajibi ne duk wanda ya yi imani da Allah ya fito ya goyi bayan wannan yunƙuri nasa domin Allah ya gargaɗi manzo kansa da cewa

Q6:159 “Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin komai: abin sani kawai al’amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa’an nan Ya ba su labari game da abin da suka kasance suna aikatawa”.

Amma malaman izala, irinsu Marigayi Jafar suna ba da fatawar cewa gara ɗan bidi’a da wanda ya ce ba ya wata ƙungiya, wato irinmu. Wasu Malaman nasu kuma na cewa ɗan bidi’a kafiri ne ko gara kafiri da shi. 

Ahmad Gumi, a ƙoƙarinsa na dawowa daga rakiyar rashin haɗin kai da nesantar juna, ya tuna mana da:

Q3:103 “Kuma ku yi riƙo (gamgam) da igiyar Allah gabaɗaya, kuma kada ku rarraba”

Amma sai ga shi wasu daga cikin masu wancan tsatstsauran ra’ayin da ake son a yaƙa sun fara kiransa da munafiki da munanan kalamai. Duk wata ƙungiya da kake taƙama da ita, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama) bai san ta ba, Khalifofin musulunci uku ba su sanar ba domin sai a lokacin Sayyadi Ali sannan aka fara samun ‘yan Shi’a da Khawarijawa. Ba a ce kar ka yi ƙungiya idan ka zaɓi hakan ba, amma dai ka san cewa Annabi bai san sunan ƙungiyarka ba, musulunci kawai ya sani, kuma musulmi wajibinsu ne su haɗa kai, matuƙar suna son dawo da martabarsu da aka sansu da ita.

Shin bai ishe mu misali ba yadda musulman duniya a yau muka zama tsintsiyar da bata shara? Mu ne na biyu a yawan Mabiya bayan Kirista, mu ne ƙungiya ta biyu (OIC) bayan Majalisar Dinkin Duniya (UN) a yawa, ga faɗin ƙasa da alabarkatu, amma a banza? Wallahi ba musulmi, ko kafiri ake wa kisan kiyashi da azabtarwar da Israila ke wa Falasdinawa, ya ci a ce musulmi sun tsayar ballantana ‘yan uwansu.

Wallahi da kan mu a haɗe ya ke, ƙarƙashin 24 ƙasashe shida kawai na tekun pasha sun isa su bayar da umarnin tsai da wannan yaƙi. Amma ina, ƙasahen Saudiya da Jordan na ba da filayen jiragensu ana amfani da su saboda yaqin. Baya ga zuru da muka yi yadda a cikin shekaru ƙasa da ashirin aka kassara, Libya, Iraq, Syria da Yemen yanzu kuma ana kan Faltsinu.

Ko mu a nan arewacin Nijeriya, mun fi kowa yawa, da albarkatu da arzikin ƙasa amma mun mai da kanmu mafiya talauchi da jahilci. Boko Haram, satar mutane da satar biro sun gama kassara mu. Wallahi idan ba mu tashi yanzu mun watsar da banbance-banbance na banza da ke tsakaninmu ba, mun rungumi abubuwa da su haɗa mu waje guda, haqiqa za mu wayi gari sai komai ya gagare mu a Arewa.

Ahmad Gumi, ina jinjina maka, kuma Allah ya ƙarfafi ƙudirinka ta hanyar sauran malamai yan uwanka daga kowacce ƙungiya masu kishin Musulunci ba ƙungiyanci ba su amsa wannan kira naka. Jazukumullah.

Sadiq marubuci ne kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ne. Ya rubuto ne daga Kano.