Allah Ya yi wa ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello rasuwa

A yammacin jiya Talata Allah Ya yi Muhammadu Bello (Wazirin Tambuwal) rasuwa.

Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun ƙanin marigayin kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, CFR, (Mutawallen Sakkwato).

Sanarwar ta nuna Marigayin ya shafe shekaru 37 riƙe da muƙamin Wazirin Tambuwal tun bayan da ya gaji mahaifinsu, Alhaji Umar Waziri Usmanu.

Kazalika, sanarwar ta ce da safiyar Larabar nan za a yi janai’zar marigayin.

Gwamna Tambuwal

A ƙarshe, Mutawallen Sakkwato ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, kana Ya sanya Aljannar Firdausi ita ce makomarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *