*Maina zai shafe shekara takwas a gidan kaso
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara takwas da aka yanke wa tsohon Shugaban Kwamitin Kula da Fansho, Abdulrasheed Maina kan yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen fansho Naira biliyan 2.1.
Alƙalan da suka saurari shari’ar, baki ɗaya su ukun sun yi ittifaƙi kan tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina kamar yadda Mai Shari’a Okon Abang ya karanto.
Jagoran alƙalan, Elfreda Williams-Daudu, ya tabbatar da hukuncin da Babbar Kotu ta yanke wa Maina ɗin wanda a kan haka shi Maina ya ɗaukaka ƙara.
Alƙalin ya ce an yi wa Maina adalci wajen sauraron shari’ar. Haka nan, ya ce mai tuhuma ya gabatar da hujjoji gamsassu.
A Nuwamban 2021 aka yanke wa Maina hukuncin zaman gidan yari na shekara takwas bayan da kotu ta kama shi da laifin tafka almundahana.