Daga BASHIR ISAH
Hukumar EFCC ta cika hannu da Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati.
Majiyarmu ta nuna Idris ya faɗa a komar jami’an EFCC ne da yammacin Litinin a Kano sannan suka ɗauke shi zuwa Abuja don ya amsa musu tambayoyi.
Majiyar ta ce kafin wannan lokaci da ma EFCC na bincike kan batun karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati da aka zargi Idris da aikatawa ta hanyar amfani da wasu kwantiragi.
Sakamakon bincike ya nuna kamfanonin da aka yi amfani da su wajen aiwatar da kwantiragin na da nasaba da ahali da abokan mu’amalar Idris.
Bayanai sun nuna EFCC ta sha gayyatar Mista Idris don ya amsa mata tambayoyi amma ya ƙi zuwa.
“Mun sha gayyatarsa amma yana ta kaucewa. Ba mu da wani sauran zaɓi face mu tsare shi,” in ji majiya daga EFCC.
A ranar 25 ga Yunin 2015 ne Shugaba Buhari ya naɗa Mista Ahmed Idris a matsayin Akanta-Janar, sannan ya sake naɗa shi a wa’adi na biyu a 2019.