Almundahana: Ana zargin Ganduje da karkatar da N51bn mallakar ƙananan hukumomi

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Rashawa da Sauraren Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, ta shigar da sabuwar ƙara kan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, inda take zarginsa da karkatar da maƙuden kuɗi Naira Biliyan 51.3 mallakar ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka a cikin wani shirin da tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Talata.

A cewar Magaji, bincike ya gano wasu kuɗaɗe mallakar ƙananan hukumomi har biliyan N51.3 wanda aka karkatar da su zuwa asusun ajiyar wasu ɗaiɗaikun mutane ba a bisa ƙa’ida ba a zamanin gwamnatin Ganduje.

Haka nan, ya yi zargin cewa, gwamnatin Ganduje ta ciri kuɗi Naira biliyan 1 duk wata daga asusun jihar kafin ƙarewar wa’adin shugabancinsa a watan Mayun 2023 da sunan gyara hanya, maimakon haka sai aka karkatar da kuɗin zuwa ga kamfanonin canji.

Kazalika, ya taɓo batun wani biliyan N4 da aka tura cikin asusun wani kamfanin harkokin noma a Kano.

Ya ƙara da cewa, “Abin da ke faruwa yanzu somin-taɓi ne kawai. A yanzu da nake wannan zancen, muna bincike kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi biliyan N51.3 wanda aka cire daga asusun gwamnati sannan aka tura cikin asusun wasu ɗaiɗaikin mutane.

“Mun shigar da ƙararraki da dama ciki har da batun Naira biliyan 1 da aka cire daga asusun gwamnati a watan Afrilun bara da sunan gyaran hanyoyi guda 30 a birane, amma sai aka tura kuɗin ga kamfanin canji,” in ji shi.