Almundahana: EFCC ta sake raba Diezani da Dala milyan $153

Daga WAKILINMU

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta sanar da ƙwato Dala milyan $153 daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke, wadda ta tsere zuwa Ƙasar Birtaniya a 2015.

Jaridar Vanguard ta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun ƙwace aƙalla kadarori 80 da kudinsu ya kai Dala milyan $80.

A cewar Abdulrasheed, “Muna fatan ganin lokacin da, wataƙila, za ta shigo ƙasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu ɗauka nan gaba. Tabbas ba mu yi watsi da batunta ba.”

Ya shaida wa manema labarai cewa a shirye yake ya sauka daga kan muƙaminsa na jagorancin EFCC idan wani ya sa shi aikata abin da bai dace ba.

Alison-Madueke ita ce ministar man fetur daga 2010 zuwa 2015.

Ta musanta aikata ba daidai ba lokacin da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi zargin cewa Dala bilya $20 na man fetur sun ɓata a ƙarƙashin shugabancinta.