Almundahana: Yadda muka cafke ministar da ta sayi gida na Dala milyan 37.5 ta bayan fage – EFCC

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya labarta yadda wata minista ta sayi gida na maƙudan kudi Dala milyan $37.5 daga hannun wani banki sannan ta biya rabin kuɗi Dala milyan $20 kuɗi hannu.

Bawa ya ba da wannan labari ne ba tare da ya bayyana sunan ministar da lamarin ya shafa ba, haka ma bai bayyana ko har yanzu ministar na kan kujera ko kuwa a’a ba.

Shugaban EFCC ya yi wannan bayanin ne yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels. Inda ya ce mahandama na narka dukiyoyin da suka wawushe ta hanyar sayen gidaje.

Bawa ya bayyana fannin gina rukunnan gidaje a matsayin fannin da aka fi zuba kuɗaɗen sata a ƙasar nan.

A cewarsa, “Ɗaya daga cikin matsalolin da muke fuskanta a ƙasar nan ita ce harkar samar da gidaje. Kashi 90 zuwa 100 na dukiyoyin da aka wawushe ana tafiyar da su ne wajen gina rukunnan gidaje. Duk da dai akwai dokoki da ke sanya musu idanu amma harajin da suke bai wa gwamnati bai kai yadda ya kamata ba.

“Mun binciki wani batu game da yadda wani shugaban banki ya sayar wa wata minista da gida kan kuɗi Dala milyan $37.5m. Bayan haka sai bankin ya tura mota ta ɗauko tsabar kuɗi a gidan ministar har Dala milyan $20 a tashin farko.

“Bankin ya samu nasarar shigar da harƙalar cikin bayanansa sannan ya biya wanda ya yi aikin ginin daga nan sai aka nemi wani lauya da ya tsaya a matsayin shi ne asalin mai gidan.”

Bawa ya ce ba don taimakon ma’aikacin ba ki ba, ministar ba za ta iya shiga wannan harƙallar ba balle ta yi facaka son ranta.