Almundahanar miliyan 950: Kotu ta wanke Alhaji Aminu Wali

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Kano, ta wanke tsohon Ambasadan Najeriya a Sin, Alhaji Aminu Wali, bisa zargin da ake masa na badakalar zunzurutun kudi har Naira Miliyan 950.

An dai gurfanar da tsohon Ambasadan ne, tare da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da wani kwamishinan sa, Dr Mansur Ahmed a gaban kuliya, bisa zargin sun yi almundahana da kudaden kamfen da shugaba Jonathan ya damka musu a shekarar 2015.

Sai dai har ya zuwa yau, ba mu da cikakken bayani a game da sauran mutum biyun da ake zargi da wannan almundahana.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*