![](https://manhaja.blueprint.ng/wp-content/uploads/2024/12/Bandit-Bomb-696x423-1.jpg)
Daga BELLO A. BABAJI
Mutane sun shiga fargaba a yankin Masarautar Ɗan-Sadau dake ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara sakamakon samun labarin cewa ƴan bindigar da suka addabe su sun fara amfani da boma-bomai wajen ayyukansu.
Wani mazaunin yankin mai suna Bello Ɗan-Sadau ya bayyana cewa, sabon salon da ƴan ta’addar ke amfani da shi abu ne mai matuƙar haɗari.
Ya ce ƴan ta’addar sun yi yunƙurin kai hari ne a ƙauyen Ƴar Galadima a safiyar ranar Lahadi, saboda haka ne suka dasa boma-boman don kare ɗaukin da jami’an tsaro ka iya kawo musu.
Ɗan-Sadau ya ƙara da cewa, an gano haka ne a lokacin da ɗaya daga cikin boma-boman ya tashi wata mota wadda a nan take ya kashe direbanta tare da ɗaiɗaita ta baki ɗaya.
Ya ce wannan shi ne karo na farko da suke ganin irin haka ya faru daga cikin munanan ayyukan ƴan ta’adda a yankin.