Al’ummar ƙasashen Turai na ɗanɗana kuɗar rikicin Rasha da Ukraine

Daga LUBABATU LEI

Yau kusan watanni shida ke nan, tun bayan ɓarkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine. Sakamakon rikicin, kamfanonin samar da makamai da na hatsi na Amurka sun ci ƙazamar riba, a yayin da kamfanonin samar da makamashi ma ba su so a bar su a baya.

Bayanai na nuna cewa, sakamakon yadda ƙasashen Turai suka biyewa ƙasar Amurka wajen ƙaƙaba takunkumai kan Rasha, yanzu haka, ƙasashen Turai da dama na fuskantar matsalar karancin makamashi mai muni, hakan ya tilasta musu sayen iskar gas daga wajen Amurka a kan farashi mai tsada, matakin da ya sa kamfanonin samar da makamashi na ƙasar Amurka cin kazamar riba, inda kusan kowane jirgin dakon iskar gas na kamfanonin Amurka da ke zuwa Turai, na iya cin ƙazamar ribar da ta kai dala miliyan 100.

Abin takaici shi ne, a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin wutar lantarki da yadda aka ƙayyade wutar da ake samar musu, al’ummar ƙasashen Turai su ne suke ɗanɗana kuɗar rikicin.

Kwanan nan ne, zanga zanga ta ɓarke a birnin Prague, babban birnin ƙasar Czech, inda kimanin mutane dubu 70 suka bazama kan tituna suna kira ga gwamnati da ta ɗauki matakai na shawo kan saurin hauhawar farashin makamashi, tare da sukan gwamnati a kan manufarta ta yin biyayya ga ƙasashen yammaci wadda ta illata moriyar ƙasar.

Kwanan baya, shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya sake sanar da samar da gudummawar soji da za ta kai darajar kusan dala biliyan 3 ga ƙasar Ukraine.

Kafin wannan, Amurkar ta samar da gudummawar soji a kalla dala biliyan 10.6 ga Ukraine.

Kamar yadda tsohon ɗan majalisar dokokin ƙasar Burtaniya, George Galloway ya fada ne, “Kamar dai yadda Amurka ke son ganin Ukraine ta yi ta yaki har sai a karshe ta faɗi ƙasa warwas, haka ta shirya ganin durƙushewa Turai.”

Amurka dai ta tada rikicin tsakanin Rasha da Ukraine, ta kuma rika rura wutar rikicin, amma ta koma gyefe tana cin riba a fakaice.

Nan ba da dadewa ba, za a shiga lokacin hunturu a Turai, amma ko ƙasashen Turai za su ci gaba da ɗanɗana kuɗar sakamakon rikicin?

Mai Zane:Mustapha Bulama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *