Al’ummar Afirka ba su buƙatar a yi musu lacca

Daga LUBABATU LEI

Ta hanyar amfani da tashoshin sadarwa na wayoyin salula da manhajojin waya da yanar gizo da dai sauransu, bisa fasahohinta na zamani, Amurka ta daɗe da yi wa gwamnatocin ƙasa da ƙasa da kamfanoninsu da ma al’ummarsu leken asiri, ciki har da ƙasashen Afirka, muna iya cewa, ta amsa sunanta na babbar ɓarauniyar satar bayanai.

Sai dai a kwanan nan, barauniyar ce take sake yin kiran a kama barawo, inda mataimakiyar sakataren harkokin wajen ƙasar ta Amurka Wendy Sherman a ziyararta a nahiyar Afirka, ta ce wai, yadda wasu ƙasashen Afirka suka zabi kamfanin Huawei na ƙasar Sin a matsayin kamfanin dake samar musu hidimar sadarwa, na nufin sun yi watsi da ikon mulkin ƙasashensu.

Lallai, ƙasar da ta saba da sata tana kuma zaton sauran ƙasashen ma barayi ne. Domin neman lalata hulɗar da ke tsakanin Sin da Afirka, Amurka ta sha gurbata gaskiya tare da shafa wa ƙasar Sin bakin fenti.

Sinawa kan ce, “Sai wanda ya sa takalma ne ya san ko sun dace.” Jama’ar Afirka sun san wace ce aminiyarsu, ba su buƙatar a yi musu lacca game da wanda ya kamata su yi hadin gwiwa. Shawarar da za mu ba Amurka ita ce, ta ba da haƙiƙanin taimako ga ƙasashen Afirka don samun ci gabansu.

Mai Zane:Mustapha Bulama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *