Al’ummar Afrika ba za su taɓa mantawa da aminiya ta ƙwarai ba

Daga FA’IZA MUSTAPHA

A baya-bayan nan ne kamfanonin ƙasar Sin suka buɗe cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da ilimin zirga-zirgar jiragen ruwa ta farko, a birnin Djibouti City na ƙasar Djibouti, da nufin inganta ƙirƙire-ƙirƙire na zamani da bunƙasa cinikayya ta intanet tsakanin ƙasa da ƙasa.

Abun sha’awa shi ne, an kafa cibiyar ne ba don riba ba, da nufin inganta ƙwarewar matasa da koyar da su dabarun shugabanci da ilimin sana’o’i da dabarun tafiyar da kamfani da sauransu.

Kamar yadda aka sani, matasa su ne ƙashin bayan al’umma, kuma horar da matasa na da ɗimbin alfanu da ba zai misaltu ba.

Dogaro da kai ko samun abun yi a wajen matashi, abun alfahari ne matuƙa, kuma zai magance kusan dukkan matsalolin da ake fama da su yanzu haka.

Idan muka yi nazari, za mu gano cewa, tushen matsalolin da ake fama da su na alaƙa mai karfi da zaman kashe wando tsakanin matasa, don haka, da zarar matasan sun samu abun yi, waɗannan matsaloli za su kau, lamarin da zai kai ga samar da ingantacciyar al’umma da ingantattun shugabanni a gobe.

Kusan duk matashin da zan gani a ƙasar Sin yana da sana’a, lamarin da nake alaƙanta shi da ci gaban da ƙasar ta samu da kuma zaman lafiyar da al’ummarta ke mora.

Kafa wannan cibiya ya zo a kan gaba, domin matasa da dama na da basira da tunani, sai dai ba su san yadda za su aiwatar da shi ba. Don haka, koyo daga ƙwararru kuma gogaggu na ƙasar Sin, haƙiƙa kyakkaywar dama ce ga matasan Afrika.

Duba da cewa, da an kira ƙasar Sin a ƙasashenmu, abu na farko da ake tunani shi ne kasuwanci.

Bugu da ƙari, irin waɗannan abubuwa da Sin da al’ummarta ke yi ba don riba ko wata ɓoyayyar manufa ba, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata fahimta da kara danƙon zumunci tsakaninta da ƙasashen Afrika, har su kasance tamkar ’yan uwa na jini a nan gaba, domin al’ummar Afrika ba za su taba mantawa da aminiya ta ƙwarai ba.