Al’ummar Arewa-maso-gabas sun roƙi Buhari da ya inganta tsaron yankinsu

Buhari

Daga UAMR M. GOMBE

‘Yan gudun hijira a yankin Arewa-maso-gabas sun roƙi gwamnati da ta taimaka ta maido da zaman lafiya a yankinsu domin ba su damar komawa gidajensu don ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba a can baya.

‘Yan gudun hijirar sun koka kan yadda rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita su tare da jefa su cikin mawuyacin halin rayuwa, lamarin da ya sa suke shakku kan ko gwamnatin za ta iya maida su matugunansu na asali.

Wata sanarwa da ‘yan gudun hijirar suka fitar a ƙarkashin Taron ‘Yan Gudun Hijira na Yankin Arewa-maso-gabas wadda Manhaja ta mallaki kwafinta, waɗanda lamarin ya shafa sun nuna damuwarsu kan halin rashin tsaron da ƙasa ke fuskanta.

Sun ce sun yi zaton samun sauyin manyan hafsoshi hakan zai haifar da canji wajen samun ingancin tsaro amma sai saɓanin haka suke gani.

Sanarwar wadda ta samu sa hannun wakilan ‘yan gudun hijirar irin su Alhaji Umar Shafa daga Barno, Chief Bitrus Waja daga Adamawa, da kuma Malam Mohammed Buni daga Yobe, ta roƙi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan ya matse ƙaimi wajen inganta sha’anin tsaro domin dawo da zaman lumana a yankunansu.

A cewarsu, “Mun yi wannan saƙo ne domin bayyana mawuyacin halin da muke ciki dangane da sha’anin tsaro a yankinmu na Arewa-maso-gabas. Musamman kuma abin da ya shafi ‘yan gudun hijira a yankin waɗanda kullum damuwarsu sai ƙaruwa take.

“Zaton da muka kyautata na yiwuwar komawa gidajenmu sai dakushewa yake kulli yaumi ba tare da wata alama da ke nuni da samun daidaito ba. ‘Yan Boko Haram sun ɗauki wani sabon salon kai hare-harensu inda sukan kai hari kai tsaye kan ƙauyuka manoma da ‘yan kasuwa.

“Wannan kuwa mataki ne da suka ɗauka da gangar domin kassara tattalin arzikin yankin Arewa-maso-gabas. Ana kashe manoma da dabbobinsu ko sace su.”

Daga nan, sun nuna godiyarsu ga Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum wanda ke bakin ƙokarinsa wajen kwatanta shugabanci abin koyi, tare da bada tabbacin cewa za su ci gaba da ba shi haɗin kai da kuma yi masa addu’ar gamawa lafiya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*