Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau, Jaridar Bleuprint Manhaja za ta yi duba ne kai tsaye zuwa ga asalin ƙabilar Nufawa da yadda suka fara rayuwa bayan isowarsu ƙasar Nijeriya da kuma kafuwar Masarautarsu.

Nupe wasu ƙabilu ne da suke rayuwa a tsakiyar Nijeria kamar su Jihar Neja, Jihar Kwara, Jihar Kogi da Abuja, Hausawa suna kiransu da suna Banufe (ɗaya) ko Nufawa, wato masu yawa kenan.

Maƙwaftansu Gwarawa suna kiran su da suna Anupeyi, kuma Yarbawa suna kiran su da suna Tapa (Takpa).

Akwai wasu yaruruka sama da biyar wadda su ke ƙarƙashin Nufawa wato Kakanda, Dibo, Kupa, Gana Gana, Bassa Nge (Nupe Tako) wato su Nufawa na kudu masu zama a ƙasar Kogi.

Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa ‘Tarihi da Al’adun Mutanen Nijeriya’ cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda ya ce, asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede ya yi gudun hijira tare da kafa masarautar Nufe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bida, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.

Amma binciken Dr. Sidi Tiwugi Shehi ya kawo ra’ayoyin masana da yawa saɓani da wannan. Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani Balarabe ne mai suna Ukba bin Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta Larabawa tare da zama a ƙasar Nufe.

Har ma Clapperton ya ce, sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nufe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara. Shi kuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamurai. Inda ya ce, zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu), amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna ‘Social Symbiosis and Tribal Organisation’.

Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nufe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata. Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka kafa birnin Kutigi.

Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.

Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nufe.

Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nufe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah (A.S). Wannan ya sa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nijeriya sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamurai, Nufawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbagyi.

Alƙalin Gwari Ummaru ya ruwaito cewa, farkon labarin Fulanin Nufe ya soma ne da Malam Dando, wanda ya zo ƙasar Nufe daga ƙasar Hausa. An ce shi mutum ne matsakaici wajen tsawo da haske, ba shi da kaurin jiki kuma. Ya iske Nufe a zamanin da Sarki Majiya ke mulki. Sai ya zama almajirinsa. A zamanin da Malam Dando ya zo ƙasar Nufe yana da ’ya’ya uku, Majigi, Abdu Vuya, da Etsu Usmanu. Ya riƙa yawo garuruwan Nufe yana wa’azi har ya isa Daba.

A wannan garin kuwa akwai wata mahaukaciya tana ɗaure cikin mari, ana kiranta da suna Fatsumako. Masu magani sun yi har sun gaji ba tare da ta samu sauƙi ba. Rannan Malam Dando na shigewa inda ta ke sai ta yi qara har ya jiyo muryar ta, sai ya tambaya cewa, “wane ne ya ke ƙara haka?” sai aka ce masa wata mahaukaciya ce wadda masu magani suka kasa warkar da ita.”

Sai Malam Dando ya ce, “ku ba ni ita zan warkar da ita, idan Allah ya yarda”. Da waliyanta suka ji sai suka amsa masa da cewa, “mun baka ita”. Malam Dando ya koma gida ya yi rubutu a alluna biyu, ya wanke, ya zuba a cikin ƙoƙuna biyu ya aika musu. Ya ce, ƙwarya ɗaya a yi ma ta wanka da ita. Ɗayar kuwa a ba ta ta sha. Sannan ya haɗa musu da turare na hayaƙi da za a yi ma ta turare da shi.

Iyayenta suka aikata kamar yadda manzon Malam Dando ya sanar musu. Da aka kwana uku sai Malam Dando ya tafi don ya ganta, sai ya ce da iyayen ta, “ku kwance ma ta marin nan”. Iyayenta suka yi wa Malam Dando musu kaɗan, sannan daga baya suka yarda suka kwance ta. Malam Dando ya kai ta cikin kafe ya ce, ta zauna nan. Daga baya sai ya nemi aurenta suka amince masa, bayan sun yi aure ya tafi da ita Juguma suka kwana ɗaki ɗaya. Daga nan bata sake komawa cikin halin hauka ba. Ta sami cikin ɗa Mustafa, sannan ta haifi Muhammadu Saba.

A zamanin da ta haifi Muhammad Saba sai sarki Majiya Zubairu ya ce yana sonsa, don haka abar shi a hannunsa ya girma. Akwai wata rana da Sarki Majiya ya shirya zuwa yaƙin Kukuku, Malam Dando ne ya ba shi asiri ya kai ya zuba a cikin ƙasar, sannan ya ci su da yaƙi ya samu dukiya mai tarin yawa. Daya komo gida sai ya aikewa Malamin kuyangi guda biyu a matsayin kyauta.

Malam Dando ya karɓe su ya yi godiya, ɗaya ya mayar da ita sa fakansa, ita ce Habibatu, ɗaya kuma ya aikewa Atiku ɗan Shaihu Usmanu, hasken zamani, kogin talikai, babban waliyi, ita ce ta haifi Ummaru Nagwamatse. Wannan duk an yi shi ne bayan rasuwar Sarkin Musulmi Muhammad Bello ɗan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Sana’ar Nufawa:
Yawancin Nufawa manoma ne. Nufawa an fi sanin su da numar shinkafa, Doya da wasu kuma kama kifi ne sana’arsu a wuraran Kogin Neja.

Kafuwar Masarautar Nupe da jerin sarakunanta:
Mai Martaba Etsu Nupe, kuma Birgediya Janar Alhaji Dakta Yahaya Abubakar mai ritaya GCFR, shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Neja.
An haife shi daga zuri’ar Marigayi Alhaji Abubakar Saganuwa Nakodin Nupe, ɗan uwan Etsu Nupe na 11, Marigayi Malam Musa Bello, mahaifiyarsa ita ce Marigayiya Hajiya Habiba Bantigi Ndayako ’yar Etsu Nupe na tara, sannan ’yar uwar Etsu Nupe Marigayi Alhaji Ummaru Sanda Ndayako, Etsu Nupe na 12.

Etsu Nupe da harshen Hausa na nufin Sarkin Nufawa, amma an fi saninsa da Etsu Bida, wanda kusan ita ce cibiyar Nufawa.

An haifi Alhaji Yahaya Abubakar ranar 12 ga Satumbar 1952, a garin Bida, daga tsatson Sanganuwar Nakordi, gidan Usman Zaki. Mutum ne mai bin tafarkin Addinin Musulunci, tsohon soja kuma Basarake.

Tsohuwar masarautar Nufe an ƙirƙire ta ce a yankin Arewa ta Tsakiya a ƙarni na 15, tsakanin kogin Neja da Kaduna wadda yanzu ta zama tsakiyar Nijeriya.

Sarki Jibrin wanda ya rayu a shekarar 1770, shi ne sarkin ƙasar Nufe na farko.

Etsu Mu’azu wanda ya gaji Etsu Jibrin da ya ɗaga darajar masarautar ya rasu a 1818, a lokacin Fulani na da matuƙar qarfi a yankin Arewacin Nijeriya, bayan rasuwar Etsu Mu’azu a lokacin ana yaƙi, daga bisani masarautar ta dawo ƙarƙashin masarautar Gwandu. Masaba, wanda da ne ga Malam Dendo daga tsatson Fulani mahaifiyarsa kuma Banufiya ce ya samu nasarar riqe masarautar a shekarar 1841.

Bayan samun nasarar haɗin gwiwa, Masaba ya yi haɗin gwiwa da Etsu Nupe Usman Zaki suka samu nasarar tafiyar da masarautar inda Usman Zaki ya jagoranci masarautar a garin Bida.

Bayan rasuwarsa a shekarar 1859, Masaba ya jagoranci masarautar har zuwa 1873, a lokacin jagorancisa, Masaba ya kafa masarautar Bida a matsayin masarauta mai ƙarfin ikon faɗa a ji mai ƙarfin soja, ya faɗaɗa masarautar ta kusurwar kudu da yamma zuwa makwaftansa inda ya cigaba da mulki har zuwa 1897, bayan zuwan Turawan Birtaniya suka ɗaga darajar masarautar.

Za mu cigaba a mako na gaba in sha Allahu.