AMAC: Candido ya ɗauki nauyin karatun yara 29

Daga AISHA ASAS

Shugaban Hukumar Abuja Municipal (AMAC) Abdullahi Adamu Candido, ya yi alƙawarin bada tallafin karatu na musamman ga ɗaliban firamare su 29 da suka shiga gasar baje fasahar rubutun insha’i na bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya na 2021 da kuma ƙaddamar da littafi wanda ya gudana a sakatariyar Hukumar Makarantun Firamare (LEA) da ke Wuse, Abuja.

Shugaban ya sanar da haka ne a wajen wani taron bita ga manema labarai wanda ya gudana a Keffi, Jihar Nasarawa.

Candido ya ce tuni an ware kuɗi naira milyan N26 domin cika wannan alƙawari da ya ɗauka na bada tallafin karatu ga ɗaliban da lamarin ya shafa.

Ya ce yayin bikin, ya nusar da yaran cewa zagewa da karatu haiƙan shi ne zai ba su damar zama abin da suke burin zama a rayuwa amma ba matsayi ko arzikin iyayensu ba.

Haka nan ya buƙaci Sakatariyar LEA da ta ɗauki lamarin gasar rubutun insha’in a matsayin abin da za ta riƙa aiwatar a-kai-a-kai domin bai wa yara daga ƙauyukan birnin tarayya damar cin moriyar shirin.

Yayin ƙaddamar da littafin mai taken “The Motor Boy”, Candido ya nuna buƙatar da ke akwai da malamai da yaran kowa ya gyara ɗamarasa tare da yin abin da ya dace.