Ambaliya: Tinubu zai gina gadar sama a mahaɗar hanyar Abuja zuwa Lokoja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirin gina gadar sama a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja domin daƙile matsalar ambaliyar ruwa.

Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana haka ne a ranar Talata, 22 ga watan Agusta, 2023, a rangadin da ya ke yi na duba ayyukan gina hanyar Abuja zuwa Lokoja, kwana guda bayan ƙaddamar da shi minista.

Ministan tare da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da wasu daraktoci a ma’aikatar sun ziyarci wasu wuraren aiki a kan hanyar.

A cewar ministan, hanyar Abuja zuwa Lokoja wata babbar ƙofa ce da ta haɗa yankunan kudu maso yamma, kudu maso kudu da kudu maso gabas da babban birnin tarayya da kuma arewacin ƙasar.

Ya ce, don haka ya kamata a ba ta fifiko saboda muhimmiyar rawar da take takawa a rayuwar al’umma da tattalin arzikin qasa.

“Mun ga yankin da a kodayaushe ke samun ambaliya a sashin Koton Ƙarfe kuma mafita ɗaya tilo da za a bi a kai shi ne a yi gadar sama a kan ta domin ta tashi sama da matakin ambaliya.

“Hakan zai yi aiki da gaske saboda yana da nisan kilomita 1.6 wanda zai ɗauki gadar sama guda biyar, kun sani, ninka ta biyu.

“Don haka za mu ba da shawara mu miƙa wa shugaban ƙasa don ya ba mu ra’ayinsa saboda muna neman mafita ta dindindin ga matsalolinmu,” in ji shi.

Ministan, ya buƙaci ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin hanyar da su yi amfani da kankare, ya ƙara da cewa za a yi nazari tare da sake fasalin kwangilar hanyoyin.

Ya yi alawarin isar da titunan siminti a faɗin ƙasar, inda ya ce sun fi dorewa kuma za su iya wuce shekaru 50 sannan kuma ba su da aikin gyara.

A nasa jawabin, gwamnan na Kogi ya yabawa ministan bisa zabar ziyarar jihar a matsayin aikin sa na farko, ya kuma yi alƙawarin bayar da dukkan goyon bayan da ya dace ga ministan da ’yan kwangilar da ke kula da hanyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *