Ambaliyar ruwa: Ɗantata, Abdussamad da sauran al’umma sun haɗa tallafin Naira biliyan ɗaya a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Hamshaƙan ‘yan kasuwa kuma masu taimako, Alhaji Aminu Ɗantata da Abdulsamad Isyaku Rabi’u, mamallakin kamfanin BUA Group, sun haɗa tallafin sama da Naira biliyan ɗaya ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa.

An bada tallafin ne a taron haɗa tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a ranar Asabar a birnin Dutse na Jihar Jigawa.

Ɗantata da Abdulsamad kowannen su ya bada gudunmawar Naira miliyan 200, inda gwamnatin Jigawa ta bada Naira miliyan 250, sai kuma Gwamnan Jihar, Muhammad Badaru, ya bada gudunmawar Naira miliyan 25.

Ɗantata, wanda ya samu wakilcin Alhaji Salisu Sambajo ya nuna damuwa kan yadda ambaliyar ruwa ta jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

Ya kuma yi addu’ar samun rahma ga waɗanda su ka rasu da kuma waɗanda ambaliyar ta raba su da mahallansu da gonakinsu.

A nashi ɓangaren, Gwamna Badaru ya gode wa waɗanda su ka bada tallafin, inda ya hori kwamitin rabon tallafin da ya yi gaskiya da amana wajen rabon ga waɗanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *