Ambaliyar ruwa da ƙarancin abinci a Nijeriya

Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin goron-zabi a Nijeriya musamman a yankin kudancin ƙasar sakamakon matsalar ambaliyar ruwa wadda ta haifar da cikas wajen safarar abincin daga arewacin ƙasar zuwa kudanci, al’amarin da ke ƙara jefa jama’a cikin halin ni-’yasu.

Ambaliyar wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 600 tare da raba miliyan biyu da muhallansu, ta haddasa asara ga ‘yan kasuwa da ke safarar hajojinsu daga Arewa zuwa kudanci sakamakon yadda ta mamaye hanyoyin da motoci suka saba ratsawa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a baya-bayan nan, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi nuni da cewa, ana sa ran ambaliyar za ta yi sanadiyar mutuwar mutane miliyan 19.5 da aka yi kiyasin cewa suna fama da ƙarancin abinci a ƙasar. Wani jami’in kula da ayyukan jin ƙai a Nijeriya, Mathias Schmale, ya ce, sauyin yanayi ne ke shafar miliyoyin mutane a Njeriya.

A cikin makon da ya gabata, Schmale ya ƙara da cewa, ya zanta da mutanen da suka yi asarar dukiyoyinsu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a ziyarar da ya kai Adamawa a Arewa maso Gabas da Anambra a Kudu maso Gabas.

A cewarsa, Anambra, da ke da sama da kashi ɗaya bisa huɗu na mutanen da abin ya shafa, ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni a Nijeriya fiye da shekaru goma. Ambaliyar ta kuma shafi wasu jihohin da ake noman abinci a shiyyar Arewa ta tsakiya da sauran jihohin da ke gaɓar kogi.

An ce gidaje da makarantu da shaguna da dama sun nutse. Haka kuma kayan abinci da dama irin su shinkafa, rogo, plantain, dawa da sauran su duk sun lalace. Dabbobi ba su tsira ba su ma. Mutane da yawa sun rasa matsugunansu kamar yadda yanzu haka suke a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban.

Bisa ƙididdigar da aka yi, ambaliya ta shekarar 2022 ta shafi jihohi kusan 34, ta kuma shafi sama da mutane miliyan 2.5, ta kashe sama da mutane 600, tare da tilasta wasu sama da miliyan 1.5 barin gidajensu. Sama da gidaje 200,000 ko dai sun lalace ko kuma ruwan ya kuri mutane daga ciki.

Dubban ɗaruruwan gonaki da suka haɗa da amfanin gona sun lalace. Idan aka yi la’akari da yadda ambaliyar ruwan ta bana za ta yi muni fiye da wanda aka samu a shekarar 2012 wadda ta jawo asarar sama da Naira tiriliyan biyu.

Misalin irin varnar da ambaliyan ya yi shi ne lalata gonakin shinkafa mafi girma a Nijeriya, hekta 45,000 na gonar shinkafar Olam da ke jihar Nasarawa. Wannan asarar ta kai kusan Dala miliyan 15.

Ƙananan manoma da ke da kashi 88 cikin 100 na manoman Nijeriya ne suka fi fama da matsalar. Wannan yanayin ya haifar da hatsari mai tsanani ga samar da abinci a ƙasar domin ko da ambaliya ta lafa, ƙasar na iya daɗewa ba ta koma kan ganiyarta na noma ba. Tabbas ambaliyar ruwan ta haifar ƙarancin abinci mai gina jiki.

Rahotanni na cewa, buhun masara da aka saba sayar da shi akan Naira dubu 15, yanzu ya koma Naira dubu 29, yayin da wasu ‘yan kasuwa ke cewa, muddin aka gaza ɗaukar matakin gaggawa, to akwai yiwuwar ƙasar baki ɗaya ta tsunduma cikin matsalar ƙarancin abinci.

Tuni dai Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta aika da tallafin abinci da suka haɗa da masara da dawa da garin-rogo ga gwamnatin jihar Lagos domin rage wa al’umma raɗaɗin ƙarancin abincin.

Kazalika gwamnatin tarayyar ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasar, NEMA ta tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa da kayayyakin amfanin yau da kullum har da abinci.

Gagarumar ambaliyar ruwan da ta mamaye garin Lokoja da ke jihar Kogi ta haifar da mummunan koma-baya ga zirga-zirgar motoci da ke safara tsakanin arewacin ƙasar zuwa kudanci, yayin da manyan motocin dakon-kaya suka maƙale a cikin garin na Lokoja, inda suka shafe makon ba-gaba-ba-baya.

Rahotanni na cewa, yanzu haka motocin dakon-kaya daga Jihar Kano na ratsawa ne ta ƙasar Nijar zuwa ƙasar Benin kafin daga bisani su dawo ta kan iyakar Seme domin shiga cikin Jihar Legas da ke kudancin Nijeriya.

Akwai buƙatar a taimaka wa waɗanda wannan iftila’i ta ambaliyar ruwa ya shafa. Ga da yawa daga cikinsu, buƙatar gaggawa ita ce matsuguni da abinci. Suna kuma buƙatar taimakon kuɗi, ruwan sha.

Hukumomin bayar da agajin gaggawa na Jiha (SEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) na da rawar da za su taka wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa domin rage raɗaɗin wannan lamari. Ƙungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta ƙasa da ƙasa ta cancanci yabo saboda fitar da rahoton gaggawar ambaliyar ruwa na dala miliyan 13 don ba da taimako ga waɗanda abin ya shafa a jihohi da dama.

Ya kamata sauran ƙungiyoyi da hukumomin duniya su yi koyi da wannan karimcin. Akwai buƙatar a nemo mafita ta dindindin kan wannan lamari. Misali, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da gyara manyan koguna waɗanda ke haifar da wannan ambaliya.

Ya kamata gwamnati ta ƙara gina madatsun ruwa domin samun wadataccen hayar wucewar ruwa, kuma irin waɗannan ruwan za a iya amfani da su wajen noma da kiwon kifi. Tare da isassun madatsun ruwa, manoma a Nijeriya za su iya rungumar noma cikin hanzari a kowane lokaci.

A taƙaice, ya kamata gwamnati ta taimaka wa manoma su yi noman rani don rage asarar da suke yi. Hakanan zai iya buɗe kasuwar hatsi don rage tasirin ƙarancin abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *