Daga BASHIR ISAH
Zauren Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen Kano ya nuna damuwarsa kan gargaɗin da ƙungiyar ECOWAS ta yi wa waɗanda suka yi juyin mulkin a ƙasar Nijar.
Zauren ya bayyana damuwar tasa ne yayin taron da ya gudanar a ranar Juma’a.
Cikin sanarwar bayan taro da zauren ya fitar, bayan nazari da lura da ya yi, ya kums ba da shawarari da yake ganin za su taimaka wajen samun maslaha a Nijar ba tare da amfani da ƙarfin soji ba.
Zauren ya ba da shawarar cewar, “Gwamnatin Nijeriya da kuma ECOWAS su bar wannan hanya da ta saɓa wa Demokraɗiiyya, su daina barazanar amfani da ƙarfin soja, su koma ga hanyar lumana da wayewa wadda aka gina a kan yanayin Diflomasiyya domin tallafa wa Jamhuriyar Nijar da mutanenta, wajen dawo da ƙasar zuwa tafarkin Demokraɗiyya.
“Lalle ne Majlisun Dokokin Tarayya, na Dattawa da na Wakilai, su farka, su tabbatar sun yi aikin da Kwansitushin ya ɗora masu, na tabbatar da cewa ba su ƙyale ɓangaren gudanarwa ya afka ƙasarmu a wani yaƙi maras alfanu ba.
“Ƙunyiyon Addini a wannan ƙasa, na kowanne ɓangare, su kama faɗakarwa gadan-gadan tare da jan hankali game da zaman lafiya a wannan yankin, da buƙatar lalle a ci gaba da maƙwabtaka cikin mutunci da girmamawa, kamar yadda ta ke tun tali-tali, tsakanin Nijeriya da Nijar.
“Kira ga dukkanin Al’ummar Musulmi da su dage da addu’o’i da ƙasƙantar da kai ga Allah, da neman agajinSa domin Ya karkato da zukatan shugabanninmu, su saurari shawarwari na hankali da ya-kamata, kada su afka mu cikin tarkon maƙiya da makircin su.
“Akwai matuƙar muhimmancin gwamnatin Nijeriya ta sake duba da cewa yanzu take ƙoƙarin kafuwa, sannan kuma ga barazanar tsaro ta ko’ina, waɗanda su ke ta tatse ‘yar lalitar ƙasar, kada a afka mu cikin wani rikici da za mu iya kaucewa, kawai don mu farantawa wasu ƙasashen duniya a siyasance,” in ji majalisar.
A ƙarshe, zauren ya jinjina da goyon bayan matakan diflomasiyya da a ka fara ɗauka ta hanyar aikawa da wakilai domin zama da jagororin sojan da ke riƙe da mulki a Jamhuriyar Nijar.