Amfani da tsohon kuɗi: Har yanzu bankuna a Abuja ba su bi umarnin Kotun Ƙoli ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Har yanzu ’yan Nijeriya ba su samu wadataccen sababbi da tsofaffin takardun Naira ba kwanaki bayan da Kotun Ƙoli ta bayar da umarni ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) kan cigana da amfani tsoffin takardar kuɗi daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Har yanzu dai bankunan da ke Abuja ba su nuna gamsuwarsu kam wannan batu ba, saboda har yanzu mazauna garin na fuskantar matsalolin ƙarancin kuɗi a wuraren cire kuɗi na ATM na POS.

A ranar Juma’a ne ƙotun ƙolin ƙasar ta halasta amfani da wasu tsofaffin takardun kuɗin Naira a matsayin takardar kuɗi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Ziyarar da aka kai wasu bankuna a Abuja, ya nuna cewa ba a samu tsofaffin takardun kuɗi ko sabbin ba; ba ma ko ƙananan kuɗin Naira 20, 50 da 100 da ba a sake fasalin su ba.

Wani jami’in bankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa NAN cewa bankin bai fara bayar da tsofaffin kuɗaɗen ba saboda babu wani umarni daga CBN.

A cewar jami’in, babu ma tsofaffin takardun da za mu baiwa kwastomomi kuma CBN bai fara bayar da kuɗaɗen ba.

Binciken da NAN ta samu ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta bi ƙa’ida ba ne saboda rashin samun ƙwaƙƙwarar takarda (CTC) na hukuncin da kotun ƙoli ta yanke.

A cewar wani ma’aikacin ma’aikatar shari’a ta tarayya, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, dole ne gwamnati ta samu CTC kafin ta umurci CBN ta bi hukuncin.

Ya ce, ana ƙoƙarin samun takardar daga kotun ƙoli.