Amfanin Goriba a jikin ɗan adam

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya:
Malama muna son mu san amfanin goriba musamman da a yanzu ake yin shayinta kuma ana ba shi muhimmanci har a kantuna ana sayar da ita.

Amsa:
Goriba wata bishiya ce da ta daɗe a duniya, amma an fi samun ta a ƙasashen Afrika, saboda tana da juriya na yanayi. Sunanta da Turanci ‘Doum Palm Tree’. Ta na ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya ɗan adam. Don haka ake amfani da ita wurin inganta lafiya da yin kariya ga wasu cutoci da kan addabi ɗan’adam. Daga cikin amfanin goriba akwai:-

•Ta na magance matsalolin jiri yayin da aka tafasa ta aka sha ruwan musamman a haɗa da garin habbatus sauda a tafasa su tare asha.

*Ga namiji mai rauni yawaita shan shayin goriba zai magance wannan matsalar. Haka kuma ana iya shaƙar kwallonta ake sansana shi ko kuma a ƙone ta ake shaƙar ƙwallon duk yadda aka yi yana magance matsalar jiri.

*Haka ga mai larurar hawan jini shan tafasasshen ruwan goriba amma a bar shi ya huce ba da zafi za a sha ba zai daidaita hawan jini.

•Goruba tana magance matsalar basur sosai idan aka tafasa ta da ɓawonta aka sha ruwan.

•Ga waɗanda ke da yawan kitse a jiki ko ƙiba shan shayin goriba yana dai-daita shi sannan ga mai jin nauyin jiki shi ma duk ana amfani da ruwan goriba ko kuma garin. Sai dai a tabbatar mai tsafta ne saboda sau tari mutane da sun karɓo a kasuwa sai su hau ci ba tare da la’akari da tsaftarta ba. Don haka muke cewa a tafasa sai fi inganci sannan a sha.

•Masu larurorin fitsari goriba tana kawo sauki.

•Ga wanda yake fama da yawan gajiya ya dimanci shan shayin goriba ko lemunta zai samu kuzari in sha Allahu.

•Goruba na yin maganin cushewar ciki shi ma a tafasa a sha ko kuma a yi lemonta.

•Lizamtar shan shayi ko lemon tafarnu yana rage damuwa irin wadda kan zo wa mutum ko da dalili ko babu kawai sai mutum ya tsinci kansa ko dai cikin damuwa ko ma ya ji yana jin haushin kowa.