Amfanin kanumfari ga lafiyar iyali

Daga BIKISU YUSUF ALI

Tambaya: Salam ina da tambaya kan muhimmancin kanumfari ga lafiya, musamman lafiyar ma’aurata.

Amsa: Kanumfari abu ne mai muhimmancin gaske ga lafiyar al’umma. Asalin sunansa Bahaushe ya aro shi ne daga harshen Larabci ‘ƙaranful’ amma da Turanci ana kiransa da Cloves. Kanumfari yana cikin tsiro da ake amfani da shi a duk duniya ko dai don kayan ƙamshi a abinci ko kuma sinadari ko ma magani.

Kanumfari yana ɗauke da sinadarai masu inganci da ƙara lafiyar jiki. Yana da matuƙar amfani a jiki amma in an sha shi dai-dai gwargwado saboda in ya yi yawa yana da illa musamman ga masu larurar gyambon ciki. Kanumfari yana maganin ‘fungai’ da ‘bacteria’ da nau’ukan cututtukan da ba ma iya ganinsu kai tsaye.

Daga cikin amfanin kanumfari akwai:-

· Ga namiji mai rauni yana da kyau ya jika kanumfari a ruwa yake sha a kullum zai samu ƙarfi sannan yana dawo da sha’awa.

· Ga mata masu juna biyu kuwa ana niƙa kanumfari ya yi laushi a cuɗe shi da zuma ake lasa lokaci zuwa lokaci musamman kafin a ci abinci da bayan an ci abincin.

· Mace da take yawan bushewa ba ta da ni’ima tana iya jiƙa kanumfari cokali biyu a ruwa kofi guda ta bar shi ya tsumu ta sha sau biyu kullum a rana. Bayan ta shanye sai ta mara ruwa a kan kanumfarin a haka har ya salance.

· Ga namijin da yake da rauni ana samun man kanumfari ya shafe gabansa da shi kafin a kusanci iyali da awa ɗaya.

· Yin turare da shi a gaban mace yana gyara gabanta ya tsuke shi sannan yana magance irin wari da bashi da kan fita sakamakon ƙiba ko rashin kula.

· Ana jika kanumfari ruwansa mace take kama ruwa /tsarki yana magance larurar sanyi .

· In an haɗa garin kamnumfari da garin lalli da garin bagaruwa ana kama ruwa da shi kullum sau 2 a rana yana magance cututtukan sanyi musamman wanda ake ɗauka da gyara gaban mace wadda ta buɗe ko a dalilin haihuwa ko cuta ko wani dalili na daban. Yana hana warin gaba ya tsaftace shi ya samar masa da kariya ta musamman.

· Ga mai warin baki kuwa ana tafasa kanumfari ake kuskure baki da shi. Amma in an zuba a bakin za a bar shi ya yi aƙalla minti biyar sai a zubar a yi kamar sau uku zama ɗaya. Amma sai ya huce za a fara.

· Haka ga mai ciwon haƙori shi ma ana kuskurawa ne amma in da akwai inda ya yi rami shi ana saka garinsa ne a liƙa a ramin.

· Ga mai ciwon kai ana sa kanumfari kaɗan a ruwan zafi a tafasa a sha tamkar shayi. Yana magance ciwon kai na mura da ma wanda ba na mura ba.

· Sa kanumfari a abinci yana hana abinci saurin lalacewa sannan ya ƙara masa ɗanɗano kuma ya inganta lafiya.

Don haka ya kamata a ce kowanne gida a samu kanumfari saboda ɗimbin amfaninsa. Allah ya sa mu dace.

Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu da ya shafi lafiyar iyali, yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta Page ɗina: Ilham Special Care and Treatment ko a Facebook account ɗina: Bilkisu Yusuf Ali.