Amurka ba za ta iya ɓata sunan Xinjiang ba

Daga CMG HAUSA

A kwanakin nan ne, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gabatar da abin da ake kira wai “ƙudirin dokar daƙile kisan kiyashi da ta’adanci” ta shekarar 2022, rahoton da ta saba fitarwa a kowace shekara ga majalisa, ta kuma ba da “Dabaru na hasashe, neman hanawa, da yin raddi ga ayyukan ta’addanci” a tarihin Amurka.

Inda aka sake sanya batun “kisan ƙare dangi” da batun “sanya aikin tilas” da sauran batutuwa da suka shafi yankin Xinjiang na kasar Sin a cikin rahoton.

Rahoton na shekara-shekara na shekarar 2022, wanda ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta gabatar, ya ci gaba da bin diddigin dabarun yada jita-jita, da neman ɓata sunan al’ummar jihar Xinjiang, tare da neman mayar da martani ga abin da ake kira wai “Dokar kare tilasta aikin ƙwadago ta Uygur” wadda ta fara aiki a ranar 21 ga watan Yunin wannan shekara.

Dukkansu sun yi amfani da batun kare haƙƙin dan-Adam, a matsayin wani makami na mayar da Xinjiang saniyar ware, a tsarin ayyukan masana’antun saka kaya na duniya, da haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar Xinjiang, ta yadda za a cimma burin dakile ci gaban ƙasar Sin.

A zahiri, duk wani rahoto, ko dabaru ko lissafin da Amurka za ta fitar, ba za ta iya bata sunan jihar Xinjiang ta ƙasar Sin ba. Domin abin da al’ummar duniya ke gani shi ne, jihar Xinjiang dake samun bunƙasuwa cikin aminci, da wadata ba kuma tare da wata rufa-rufa ba.

Don haka, wannan ba shi da nasaba da abin da ake kira wai “kisan ƙare dangi” da “aikin tilas”.

Mai fassara: Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *