Amurka mai iƙirarin wai tana “kare haƙƙin bil Adam”

Daga CRI HAUSA

Bayan harin “9.11” a shekarar 2001, Amurka ta ƙaddamar da yaƙi a Afghanistan da sunan “yaƙi da ta’addanci”.

A cikin shekaru 20 da suka wuce, matakan soja da Amurka ta ɗauka a Afghanistan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, a yayin da wasu sama da dubu 60 suka jikkata. Baya ga haka, kusan kaso 1/3 na al’ummar ƙasar ta Afghanistan sun kuma zama ‘yan gudun hijira.

Hakan abun takaici ne, kuma abin da ya faru a Afghanistan wani ɓangare ne kawai na matsalolin da Amurka ta haifar ga sauran ƙasashen duniya. Bisa sakamakon binciken “Tsadar Yaki” wanda cibiyar Watson mai kula da harkokin ƙasa da kasa da na al’umma ta jami’ar Brown ta fitar, yakin da Amurka ta ƙaddamar wai da sunan yaki da ta’addanci cikin shekaru 20, ya haddasa mutuwar mutane sama da 929,000.

Ban da wannan, a yayin da ake fuskantar ƙalubalen annobar Covid-19, Amurka ta yi ta ƙaƙƙaba takunkumai a kan wasu ƙasashe, matakin da ya ƙara tsananta matsalar jin kai da waɗannan ƙasashe ke fuskanta.

Lallai har kullum Amurka na ɗaukar kanta a matsayin misali a wajen kare haƙƙin bil Adam, amma kuma ga abun da take yi a zahiri.

Mai zane: Mustapha Bulama