Daga CMG HAUSA
Shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwunmi Adesina, wanda tsohon ministan noma ne a Najeriya, a yayin zantawarsa da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a kwanan baya, ya ce rikicin Rasha da Ukraine, ya haddasa hauhawar farashin alkama da kusan kaso 60 bisa ɗari a ƙasashen nahiyar Afirka. Adesina ya ƙara da cewa, tashin hankalin ya haifarwa duniya tarin ƙalubale, musamman ma ƙasashen Afirka, masu shigo da kaso mai yawa na abincin da suke buƙata daga ƙasashen biyu.
Abin haka yake, daidai kamar yadda Adesina ya ce, ɓarkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya haifar da munanan illoli ga tattalin arzikin duniya, musamman ma ƙasashen Afirka.
Amma kasancewarta ƙasar da ta hura wutar rikicin, ƙasar Amurka ta ci mummunar riba, inda kamfanoninta na samar da makamai suka ci riba bisa yawan makaman da aka saya daga wajensu.
Daga farkon shekarar 2022, sakamakon tasirin annobar Covid-19, an sha samun faɗuwar farashin hannayen jari a kasuwar hada-hadar kuɗi, amma wata guda bayan ɓarkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraien, farashin hannayen jari na manyan kamfanonin samar da makamai na ƙasar Amurka, ciki har da Lockheed Martin da Raytheon, sun yi tashin gwauron zabi.
Mai Zane: Mustapha Bulama