Amurka sarauniyar leƙen asiri ce ta duniya

Daga AMINA XU

A shekarun bayan nan, masunta Sinawa sun deɓo wasu na’urori daga teku, waɗanda ƙasashen ƙetare suka ƙera su don leƙen asiri. Hakan ya sa an tuna da yunƙurin leƙen asiri da Amurka ta yi ƙarƙashin shiri mai laƙabin “PRISM”, da shirin “Irritant Horn”, da shirin “Muscular” da dai sauransu.

Gwamnatocin ƙasashen waje da dama, ciki har da Jamus, da Faransa, da Brazil, sun yi tir da waɗannan yunƙuri na leƙen asirin da Amurka ke yi. Tabbas Amurka sarauniyar leƙen asiri ce ta duniya.