Amurka ta ƙara sata

Daga MUSTAPHA BULAMA

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Sana na ƙasar Syria na cewa, kwanan baya, sojojin da Amurka ta jibge a Syria da dakarun adawa da take marawa baya, sun ƙara satar albarkatun mai daga lardin Hasaka. Bayanai na cewa, wasu motocin sojan Amurka masu sulke sun ba da kariya ga wani ayarin motoci 50 waɗanda yawancinsu tankoki ne da ke cike da man da suka sata daga filayen mai na lardin.

Wannan ba shi ne karo na farko da sojojin Amurka suka saci albarkatun mai a Syria ba tun bayan da Amurka ta tura sojojinta zuwa Arewa maso gabashin kasar a shekarar 2015, ba tare da amincewar gwamnatin Syria mai ci ba, ta rika satar mai daga yankin. Yawan man da kasar Syria ta samar a kowace shekara ya kai kimanin ganguna dubu 85.9, amma Amurka da dakarun da take marawa baya, sun kwace kimanin dubu 70 daga cikinsu, ƙasa da ganga dubu 16 ne ya rage da za a iya samar wa a kasuwar cikin gidan Syria.

Amurka dai ta haddasa yaƙi da rikici, amma kuma ta tafi da albarkatu da arzikin da ta sata a ƙasar, wannan shi ne abin da take kira wai “dimokuraɗiyya” da “’yanci” ke nan.

Mai Zane: Mustapha Bulama