Amurka ta buƙaci kamfanonin sadarwa su dakatar da aikin fasahar 5G

Hukumomin Amurka sun nemi kamfanonin sadarwa na AT&T da Verizon da su jinkirta aikin sadarwar 5G har tsawon makonni biyu, yayin da ake ganin rashin tabbas game da katsalandan ga muhimman kayayyakin kariya na jiragen sama.

Tuni dai kamfanonin suka fitar da sanarwar cewa sun fara nazartar wannan buƙata ta gwamnatin Amurka.

A ranar 5 ga watan Disamba ne Amurka ta fitar da fasahar sadarwar wayar tafi-da-gidanka, amma aka jinkirta zuwa ranar 5 ga watan Janairu bayan da manyan kamfanonin sararin samaniyar Airbus da Boeing suka nuna damuwa game da katsalandan da na’urorin da jiragen ke amfani da su wajen auna sahihancin shirin.

Sakataren Sufuri na Amurka Pete Buttigieg da Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama, Steve Dickson, sun nemi jinkirin baya-bayan nan a cikin wata wasiƙa da aka aika ranar Juma’a ga AT&T da Verizon, manyan manyan kamfanonin sadarwa na ƙasar.

A cikin wasiƙar, hukumomin Amurka sun ba wa kamfanonin tabbacin cewa sabis na 5G zai iya farawa kamar yadda aka tsara a watan Janairu, sai dai akwai buƙatar a ba wa wasu filayen jiragen sama masu muhimmanci damar da suke buƙata.

Hukumomin ƙasar dai sun ce, akwai buƙatar kare lafiyar jiragen sama, tare da tabbatar da cewa tura 5G da ayyukan jiragen sama na iya kasancewa tare.