Gwamnatin Amurka ta ce ta ɗauki matakan haramta wa wasu ‘yan Nijeriya bizar shiga ƙasar saboda yi wa tsarin dimokuraɗiyya zagon ƙasa a lokacin zaɓuɓɓukan 2023 a ƙasar.
Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ya fitar a ranar Litinin, 15 ga Mayu, 2023, wadda aka wallafa a shafin intanet na gwamnatin Amurka.
A cewar Sakataren “A yau, ina sanar da cewa mun ɗauki matakan ƙaƙaba takunkumin biza ga wasu ‘yan Nijeriya saboda aikata zagon ƙasa ga tsarin dimokradiyya a lokacin zaɓukan Nijeriya na 2023.”
Blinken ya ƙara da cewa, “Amurka ta ƙuduri aniyar tallafawa da kuma ciyar da dimokuraɗiyya gaba a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.”
Haka nan, ya ce takunkumin bizar ya keɓanta ne da wasu mutane amma ba a kan al’ummar Nijeriya ko gwamnatin ƙasar ba.