Amurka ta zama babbar kwabo

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Amincewa da manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, ita ce tubali ko sharaɗin duk wata hulɗa da wata ƙasar waje za ta ƙulla da ƙasar Sin. Wannan dai yana nufin, amincewa Taiwan Ko Hong Kong, dukkansu wani ɓangare da ba za a iya raba su da ƙasar Sin ba.

A matsayin Amurka na wadda take kiran kanta da babbar ƙasa a duniya, ya kamata a ce tana sane da wannan ko ma in ce tana kiyaye wannan ƙa’ida. Sai dai abin kunya shi ne, yadda take ci gaba da zubar da kimarta a idon Sinawa har ma da ɗaukacin duniya. Har kullum, burin ƙasar Sin shi ne, hawa teburin sulhu, domin a daddale batutuwa, a cimma matsaya mai gamsarwa ga dukkan ɓangarori. Sai dai, duk wannan yunƙuri bai gamsar da Amurka ba, inda take gaban kanta wajen tada rikici da ƙaƙaba takunkumai da shiga sharo ba shanu, da ma duk wani nau’i na takala.

A baya-bayan nan Amurkar ta yi alƙawarin aiwatar da manufar Sin da ya taka a duniya, kuma ba za ta goyi bayan masu rajin ɓalle tsibirin Taiwan daga Jamhuriyar Jama’ar ƙasar Sin ba, amma kuma abin takaici shi ne, bayyanar shirinta a ranar Litinin da ta gabata, na cewa, za ta sayar da hidimomin tsaro da makamai ga yankin Taiwan, waɗanda darajarsu ta kai dala miliyan 100. Kuma, wannan shi ne karo na biyu da ta yi hakan.

Duk wani mai bibiyar hulɗar Sin da Amurka, ya san cewa, Amurka ba ta cika alƙawurran da take ɗauka na kyautata hulɗa tsakanin ƙasashen biyu, ko kuma tana amai tana lashewa, lamarin da ya mayar da ita babbar kwabo. Haka kuma, a bayyane yake, ba ta muradin ganin zaman lafiya da ɗinkewar ƙasar Sin. Tana sane cewa, ayyukan nata za su kawo hatsaniya, amma, ta gaza la’akari da hakan, idan ta mayar da hankali wajen cimma moriyarta, wanda kuma mumunan tasirinsa, zai shafe ta da al’ummarta.

Kamata ya yi, babba ya riƙa zama abun koyi ga na kasa da shi. Kamata ya yi a ce sabbin ƙalubalen da suke kunno kai a duniya, su zama darasi ga Amurka, na ganin an gudu tare an tsira tare, maimaikon kawo rarrabuwar kawuna.

A matsayinsu na manyan ƙasashe, kamata ya yi Sin da Amurka su zama abin koyi ga sauran ƙasashe. Ya kamata idan aka cimma yarjejeniya, to a aiwatar da ita, ba wai a riƙa saɓa alƙawari ba, domin wannan, ba zai taɓa kai duniya ga samun kyakkyawar makomar da ake buƙata ba, ko kuma zaman lafiya da fahimtar juna da ake muradi.

Ƙasar Sin dai ta sha nanata cewa, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ko gazawa wajen kare cikakken iko da yankuna da tsaro da muradun jama’arta ba. Kuma a shirye take ta mayar da martani kan duk wani yunƙuri na lalata moriyarta.