Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya buƙaci a gudanar da taron rantsar da shi a keɓantaccen waje.
Trump ya nemi hakan ne sakamakon matsanancin yanayi na sanyi mai haɗari da babban birnin ƙasar ke fama da shi.
Ya ce za a gudanar da abin da ya shafi gabatarwa da addu’o’i da jawabai a wani waje kamar yadda Shugaba Ronald Reagan ya yi a shekarar 1985.
Ya ƙara da cewa za a buɗe filin Capital One Arena a ranar Litinin don haska taron mai ɗunbun tarihi da kuma taron shugaban ƙasa, ya na mai cewa zai halarci filin bayan an rantsar da shi, kamar yadda BBC ya ruwaito.