Amurka za ta ƙara yawan dakarunta a Gabas ta tsakiya – Pentagon

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da shirin aikewa da ƙarin dakarun Soji gabas ta tsakiya don bai wa Isra’ila kariya, sanarwar da ke zuwa a dai dai lokacin da rikicin ƙasar ta Yahudu ya juye tsakaninta da Iran bayan hare-haren da Tehran ta kai mata.

Kakakin Pentagon Sabrina Singh ta ce Amurkan za ta ƙara yawan dakarun na ta zuwa 43,000 yankin gabas ta tsakiya, wanda zai ƙunshi ƙara yawan hatta kayakin yaƙinta da suka haɗa da jiragen Soji da na kai farmaki.

Tun bayan tsanantar rikicin Isra’ila da Hezbollah wanda ya kai ga kisan jagoran ƙungiyar Sayyed Hassan Nasrallah, fargaba ta baibaye yiwuwar ta’azzarar yaƙin zuwa wasu sassa na gabas ta tsakiya.

A cewar Pentagon da ma ta yi zama cikin shiri saboda abin da ka je ya zo, wanda ke nuna cewa dole ta girke ƙarin dakaru don bai wa Isra’ila kariya.

Pentagon ta bayyana cewa cikin sabuwar rundunar da za ta aike gabas ta tsakiya za ta ƙunshi tarin jiragen yaƙi da suka haɗa da nau’ikan F-15E da na kai farmaki kirar F-16, da kuma na yaƙi ƙirar F-22 kana A-10.

Ma’aikatar ta Pentagon ta ce wannan sabuwar runduna za ta isa gabas ta tsakiya ne don ƙara ƙarfi kan dakarun da tun tuni suke a yankin. RFI