An ƙaddamar da kwamitin bikin miƙa sanda ga Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya

Daga BILKISU YUSUF ALI

Ranar Asabar, 18 ga Disamba, 2021, aka ƙaddamar da kwamitocin da za su jagorancin bikin bayar da sanda na Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr) Aliyu Ibrahim Gaya (Kirmau Mai Gabas) a ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano kuma Wazirin Gaya, Alhaji Usman Alhaji.

Taron da aka yi a ɗakin taro na Africa House da ke Gidan Gwamnatin Jihar Kano, an fara shi kusan ƙarfe 3:00 na rana. Sarkin Malaman Gaya, Sheikh (Dr) Yusuf Ali ne ya buɗe taron da addu’a. Daga nan sai jagoran taron, Alhaji Usman Alhaji, ya yi taƙaitaccen bayani kan maƙasudin taron na kafa kwamitocin, inda ya ƙaddadamar da kwamitoci guda shida.

Kwamitocin su ne, kwamitin zartarwa, wanda shi ne babban kwamitin ƙoli wanda kuma shi Wazirin na Gaya zai jagoranta. Sai kwamitin kuɗi da kwamitin saukar baƙi da kwamitin yaɗa labarai da kwamitin tsaro da kuma kwamitin da zai kula da filin taro. Waɗannan kwamitoci an ƙaddamar da su kuma sun fara aiki nan take.

Ranar Asabar, 22 ga Janairu, 2022, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, suka ware, don wannan gagarumin biki na bayar da sandan girma ga Sarkin Gaya.

Shi dai wannan biki na bayar da sanda an samo shi ne bayan zuwan Turawan mulki ƙasar Hausa. Turawa sun samu dukkan limaman Ƙasar Hausa a wancan lokacin suna amfani da kandiri (sanda) suna dogarawa, musamman yayin huɗuba. Wataƙila wannan ya ba su haske wajen assasa da sanin muhimmancin sanda. Miƙa sanda na nufin shiga ofis da fara aiki gadan-gadan. Don haka ake yi wa wannan biki tanadi na musamman, don gudanar da shi. Bikin ana yin sa ne sau ɗaya a rayuwar sarki.

Waɗannan kwamitoci sun shirya tsaf, don yin aiki gadan-gadan, domin samun biki na bajinta da ban sha’awa. Allah ya taimaki Sarkin Gaya, Alhaji (Dr) Aliyu Ibrahim Gaya, Allah ya riƙa ma sa, kuma Allah ya kara masa lafiya, amin.