A halin da ake ciki, ‘yan kasuwa sun cilla farashin fetur daga N537 zuwa N617 kan lita guda a wasu gidajen mai mallakar Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL).
An ga wani gidan mai mallakar NNPC s ranar Talata a Abuja yana sayar da fetur N617 kan kowace lita.
Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren NNPC ko makamancin haka dangane da ƙarin kuɗin man.
Tun bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai baki ɗaya a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki a watan Mayu, farashin man ya cilla sama zuwa sama da N500 kan lita, sai kuma ga shi a wannan karon farashin ya sake ƙaruwa zuwa N617.