An ƙara kuɗin Hajjin bana zuwa N8m

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ce an samu ƙari a kuɗin Hajjin bana inda a yanzu maniyyaci zai biya Naira miliyan 8 domin tafiya aikin Hajjin 2024.

Sanarwar da NAHCON ta fitar ta bakin Kakakinta, Hajiya Fatima Sanda Usara a ranar Lahadi, ta ce, tsayayyen farashin da maniyyatan bana za su biya shi ne N8, 225, 464.74 ga waɗanda suka fito daga yankin Adamawa/Borno.

Fatima ta ce, “sabon biya daga yankin Arewa zai biya N8, 254, 464.74, sannan daga yankin Kudu za su biya N8, 454, 464.74.”

Ta ƙara da cewa, ana sa ran dukkanin rukunonin maniyyatan kowa ya biya ko ya cikasa kuɗinsa kafin cikar wa’adin da aka tsayar.

A cewar sanarwar, maniyyatan da suka fara biyan N4.9m da fari, yanzu za su yi cikon N1,918,032.91.

Haka nan, ta ce baki ana da maniyyata 48,414 ne daga sassan ƙasa da suka yi niyyar sauke farali a bana.

NAHCON ta ce ƙarin da aka samu na da nasaba da yanayin da Dala ta tsinci kanta a wannan lokaci.

Kazalika, hukumar ta ce ƙofarta a buɗe take domin maida wa manyyaci kuɗinsa idan buƙatar hakan ta taso.